Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta kama wata mata mai suna Kadija Yakubu mai shekara 22 da da ake zargi da kashe ƴaƴan mijinta uku.
A wata takarda da aka raba wa manema labarai a makon jiya jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Dungus Abdulkarim ya ce wannan abu ya faru ne a kauyen Makara-Huta dake karamar hukumar Potiskum.
Abdulkarim ya ce Kadija ta zuba wa yaran guba ne a cikin shayin da safe, ba da dadewa ba kuwa yaran suka fara shureshure. Cikin gaggawa a ka garzaya da su asibiti.
Ko da aka kaisu asibin uku cikin yaran sun ce ga garun ku nan, sai da ɗaya mai sauran kwana na nan shi bai rasu ba
Ya ce ƴan sanda sun fara gudanar da bincike domin gano irin guban da Kadija ta yi amfani da shi da kuma dalilin kashe wadannan yara da ta yi.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda wani magidanci Usman Sama’ila mai shekara 40 ya kashe ɗan matarsa saboda kishi, wato agolansa kenan.
Wannan abu dai ya faru a kauyen Tsakuwama dake karamar hukumar Miga jihar Gombe sannan yaron da Sama’ila ya kashe bai wuci watanni 17 da haihuwa ba.
Kakakin rundunar NSCDC Adamu Shehu wanda ya sanar da haka ya ce mahaifiyar yaron ne ta shigar da karan kisan danta a ofishin su inda ta nuna musu cewa tana zargin mijinta ne ya kashe yaron.
Shehu ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa Sama’ila ya fita da wannan yaro domin ya raka shi gona inda a gonan ne ya shake yaron har ya mutu.
Discussion about this post