Yayin da Gwamnonin Kudu su ka ce lallai mulki a kudu zai koma a zaɓen 2023, a yanzu su ma Gwamnonin Arewa sun yunƙuro da na su alayen siyasar, inda su ka ce ba za a yi tsarin karɓa-karɓar shugabancin Najeriya ba, a zaɓen 2023.
Sun ce tsarin karɓa-karɓa ya kauce wa tsarin mulkin Najeriya.
Haka nan kuma gwamnonin sun ƙi amincewa da matsayar gwamnonin kudu masu hanƙoron cewa jihohi ne ke da haƙƙin karɓar harajin jiki magayi, wato VAT, ba Gwamnantin Tarayya ba.
Gwamnonin Arewa sun fitar da wannan matsaya ta su a taron su na NGF da su ka gudanar a ranar Litinin, a Kaduna.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato, kuma ɗan jam’iyyar APC, shi ne ya bayyana wannan matsaya ta su, a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan kammala taron.
“Wasu Gwamnonin Arewa sun yi azarɓaɓin bayyana son ran su wajen nuna goyon bayan cewa a miƙa mulki zuwa shiyyar kudancin ƙasar uku, domin a ƙara ɗinke ɓaraka da ƙasa danƙon zumuncin zaman lafiya da juna.
“To wannan dai ra’ayin su ne su ka faɗa. A matsayin mu na Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, mun yi tir da sanarwar da Gwamnonin Kudu su ka fitar, inda su ka ce tilas a miƙa mulki ga kudancin Najeriya a 2023.
“Bayanin na su ya ci karo da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, wanda ya ce ɗan takara zai iya zama shugaban ƙasa, idan ya samu ƙuri’u aƙalla kashi 25% a cikin jihohi kashi 2/3 na fadin ƙasar nan.
“Idan ta kama za a je zagaye na biyu, to wanda ya fi yawan ƙuri’u shi zai yi nasara.” Inji sanarwar ta su.
Gwamnonin kuma sun goyi bayan cewa Gwamnatin Tarayya ce ke da haƙƙin karɓar harajin VAT, ba jihohi ba.
“Idan aka ce kowace jiha ta riƙa karɓar VAT, to haraji zai yi yawan da farashin abinci da sauran kayan massrufi zai riƙa tashi sosai yadda idan ya cira sama, ba za a iya cafko shi ba.”
Tuni dai jihohi biyu da su ka fi tara wa Najeriya VAT, wato Ribas da Legas sun kafa dokar hana tarayya karɓar VAT a jihohin su.
Discussion about this post