Hukumar Bunƙasa Ilmin Ƙananan Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ta bayyana takaicin yadda a cikin shekaru 12 Boko Haram su kashe malaman makarantun zamani har su 2,295 a Barno.
Cikin wata tattai musamman da ta yi da PREMIUM TIMES, Babbar Jam’iar UNICEF a Maiduguri, Phuong Nguyen ta kuma bayyana takaicin cewa tsakanin 2009 zuwa 2020 Boko Haram sun lalata makarantu 1,400 a Barno.
Nguyen wadda ta taɓa zama wakiliyar UNICEF a Somaliya, ta ce hare-haren ta’addanci sun matuƙar durƙusar da harkokin ilmi a Arewa maso Gabas na Najeriya, musamman a jihar Barno.
“An kulle dukkan makarantun Jihar Barno daga watan Disamba 2013 har zuwa Yuni 2015. Wannan ba ƙaramin koma-baya ba ne.
“Su ma jihohin Adamawa da Yobe sun fuskanci irin wannan matsala, an kulle makarantun ba su daɗe sosai kamar jihar Barno ba.”
Nguyen ta ce hare-haren dama kai-tsaye ana yin su ne domin a kassara harkar ilmi a jihohin, kuma sun yi mummunar illa wajen mayar da yankin, musamman jihar Barno koma-baya a ɓangaren ilmi.
Ta ce binciken baya-bayan nan da HNO ta yi ya nuna kashi 52% na ƙananan yaran jihar ba su taɓa zuwa makaranta ba.”
Nguyen ta ce dubban ɗaruruwan ƙananan yara na rayuwa maras tabbas a sansanonin masu gudun hijira, wasu babu iyaye, wasu kuma an tsallaka da su ƙasashe makwabta su na gudun hijira.
Ta nuna damuwar ta dangane da makomar yaran waɗanda ba su zuwa makaranta, musamman ma yara mata ƙanana.
Jami’ar ta UNICEF ta ce kisan malaman makaranta babban cikas ne wajen samar da ilmi, kuma wannan matsala ce ta ƙara haifar da taɓarɓarewar ilmi a yankin, musamman a jihar Barno.