Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya shaida cewa idan Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya fito takarar zaɓen shugaban ƙasa a 2023, zai iya yin tasiri sosai.
Sule ya shaida wa ƙungiyar Progressive Consolidation Group cewa idan aka ɗaya Osinbajo a kasuwar 2023, nan da nan za a sayar da shi la’ada waje, ba zai yi kwantai ba.
Haka ya shaida masu yayin dasu ka kai masa ziyara a Gidan Gwamnantin Jihar Nasarawa, ranar Litinin ɗin nan.
Sule ya gode masu tare da yi masu fatan alheri da kuma jin daɗi, ganin yadda su ka runtuɓe shi, su ka sanar da shi kyakkyawar aniyar su ta ganin an tsayar da Osinbajo takarar shugaban ƙasa a 2023, domin ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.
Sun nuna cewa idan Mataimaki ya gani Shugaba, to kuwa zai ɗora ne daga inda ya tsaya wajen bijiro da ayyukan alheri irin waɗanda Buhari ke yi a yanzu.
Gwamna Sule ya tabbatar masu cewa kada ma su samu wata damuwa ko kaɗan wajen bayar da ta sa goyon baya, muddin Osinbajo ya nuna buƙatar fitowa takara a zaɓen 2023.
Ya ce ai Osinbajo sahihin mutum ne, managarcin da ko kaɗan ba zai taɓa yin kwantai ba a tsakanin ‘yan takara.
“Mu dama damuwar mu ita ce yadda za a ɗora daga inda Shugaba Buhari zai tsaya. Saboda haka idan ku ka bijiro da wata mafita, to ba ni kaɗai ba, har sauran gwamnonin APC baki ɗaya, duk za za su raja’a a kan ku.
“Idan za ku tallata Osinbajo, to ko ana kwantai a kasuwar siyasa, Osinbajo ya fi ƙarfin yin kwantai”
Shugaban PSG Aliyu Kurfi, ya ce sun je rangadin neman goyon bayan gwamnan ne don raɗin kan su, ba tare da sanin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo ba.
Discussion about this post