Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kaduna, Mohammed Sani Abdullahi, ya jagoranci tawagar ƴan APCn Kwarbai a karamar hukumar Zariya, inda suka yi wa PDP Kifa-ɗaya-kwala a zaben shugaban karama da aka yi ranar Asabar.
A sakamakon zaɓen wanda shi da kansa ya saka a shafin sa, a sakamakon shugaban ƙaramar hukuma APC ta samu kuri’u 200, PDP 22, Kansila kuma APC 204, PDP 22.
PDP ta yi nasara a mazaɓar gwamna El-Rufai
Jam’iyyar PDP ce ta yi nasara a mazabar gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai wato mazaɓar Unguwwr Sarki inda a nan ne ya ke yin zaɓe.
A sakamakon da malamin zabe na wannan rumfa ya sanar ya bayyana ce PDP ce ta yi nasara a zaben kujerar shugaban karamar hukuma da na Kansila.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen Mohammed Sani, ya ce jam’iyyar PDP ta yi nasara a duka kujerun a wannan mazaɓa.
” A kujerar shugaban karamar hukumar Kadynanta Arewa APCn El-Rufai ta samu kuriu 62, PDP 86, APP 1, ZLP 5, PRP 4
” A kujerar Kansila PDP ta samu kuri’u 100 cikin kuri’u 162 da aka kaɗa, APC ta samu kuri’u 53, ZLP 2, PRP 2, NNPP 1, BP 4.
Discussion about this post