SHARI’A SAƁANIN HANKALI: Cif Jojin Najeriya zai binciki alƙalan jihohin da su ka ɗaura banten tutocin jam’iyyun siyasa

0

Babban Jojin Najeriya Tanko Mohammed ya bada umarnin buƙatar ganin kwafe-kwafen shari’un da Manyan Alƙalan Jihohi su bakwai su ka yanke, kafin su gurfana wurin binciken su da za a yi a ranar Litinin.

Tanko dai ya zargin Manyan Alƙalan da bayar da hukuncin shafe wani hukunci na baya da kotunan jihohi su ka riƙa yi, wanda ya ce lamarin ya zama abin kunya kuma abin takaici ga tsarin shari’ar Najeriya.

Alamomi sun nuna cewa cikon Mai Shari’a na bakwai da aka gayyata domin gurfana, shi ne Babban Mai Shari’a na Babbar Kotun Jihar Delta, kuma duk za su bayyana a ranar Litinin.

“Cif Jojin Najeriya ya gayyaci Manyan Alƙalan Jihohin Ribas, Kebbi, Anambra, Jigawa da kuma Imo. Za su sha tambayoyi da binciken yadda su ka bayar da wani hukunci a Manyan Kotunan Jihohin su, wanda ya shafe wani hukuncin da wata kotun ta jiha ta zartas. An nemi su bayyana a ranar Litinin, 6 Ga Satumba, 2021.”

Mai Shari’a Onome Umukoro na Delta ya jefa kan sa cikin tsomomuwa, inda ya bayar da hukuncin dakatar da zaɓen Shugabannin APC na rassan Ƙananan Hukumomin Jihar Delta, wanda aka shirya gudanarwa tun a ranar 4 Ga Satumba, 2021.

Sai ya ɗage sauraren ƙarar sai ranar 7 Ga Satumba, domin ci gaba.

Lauyoyi da dama sun bayyana wa wannan jarida cewa shari’un an tsoma dungulmin siyasa a cikin su.

Premium Times ta ji cewa shi ma Cif Jojin Najeriya Tanko Muhammad zai gana da lauyoyi a kan lamarin.

Majiya daga Hukumar NJC wadda ke da ikon naɗa Alkalai, ta ce yunƙirin da Tanko Muhammad ya yi wani ƙoƙari ne na daƙile cin hanci da rashawa a fannin shari’a, musamman a tsamarin masu shari’a.

Farkon wannan makon wannan jarida ta buga labarin cewa Cif Jojin Najeriya ya gayyaci Manyan Alƙalan Jihohi shida saboda manna wa shari’u bandejin siyasa.

Babban Jojin Najeriya Tanko Muhammad ya gayyaci Manyan Alƙalan Jihohi shida saboda samun su da aka yi sun bayar hukunci mai cike da murɗa-murɗar siyasa a kotunan su.

Muhammad wanda shi ne Shugaban Majalisar Ladabtar da Alƙalai, ya gayyace su ne a Abuja, kamar yadda PREMIUM TIMES ta samu labari.

Alƙalan da za a yi wa tambayoyi ko tuhuma su shida, sun fito ne daga jihohin Ribas, Kebbi, Cross Riba, Anambra, Jigawa da Imo.

Ana tuhumar su ne da laifin bayar da hukunce-hukunce masu ɗaure kai a kan wasu shari’u na siyasa cikin watannin nan biyu da ake ciki.

Kakakin Cif Jojin Najeriya, Ahuraka Yusuf, ya tabbatar da an aika wa manyan alƙalan sammace a ranar Litinin.

Za su yi wa Tanko Muhammad bayanin dalilin bauɗaɗɗen hukuncin da su ka riƙa yankewa a tsakanin su.

Alƙalan dai sun bayar da kai borin ‘yan siyasa ya hau, inda idan wannan ya yanke hukunci kan wani batun siyasa, gobe kuma sai wani ya soke hukuncin.

Idan ba a manta ba, makonni biyu da su ka gabata Babbar Kotun Jihar Fatakwal ta dakatar da Uche Secondus daga kiran kan sa Shugaban Jam’iyyar PDP.

Kwana ɗaya bayan yanke wannan hukunci, sai kuma Babbar Kotun Birnin Kebbi ta jingine hukuncin da kotun Ribas ta yanke.

Bayan an maida Secondus kan kujerar, sai wata kotu a Kalaba ta sake dakatar da shi. Lamarin da bai yi wa NJC daɗi ba.

Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ita ma ta nuna matuƙar damuwar ta kan wannan ɗabi’a da halayyar da alƙalan ke nunawa da ta ce abu ne mai gurgunta darajar kotuna da shari’u.

NBA ta ce ya zama wajibi Cif Jojin Najeriya ya yi wa tubƙar hanci.

Share.

game da Author