Ministan kiwon lafiya, Ehinare Osagie ya bayyana cewa sama da mutum 2000 ne korona ta kashe a Najeriya daga Faburairun 2020 zuwa yanzu.
Ƙididdigar aka buga a yau Juma’a, ta nuna cewa korona ta kashe mutum 2,671, kuma rahoton ya nuna cewa kashi 90 na waɗanda korona ke kashewa, ba su yi rigakafin korona ɗin ba.
Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA) ta ce Najeriya ta yi wa mutum miliyan 4.6 rigakafin korona allura ta farko.
Ya ce mutum 1, 875, 127 aka yi wa yi wa allura ta ta biyu.
Ministan Harkokin Lafiya Osagie Ehanire ya ce aƙalla akwai buƙatar a yi wa kashi 70 cikin 100 na ‘yan Najeriya allurar rigakafin korona.
Minista Osagie ya kara da cewa annobar Korona ta yi wa tattalin arzikin Najeriya rugurugu.
Sannan ya ƙara da cewa kashi 90 cikin 100 na waɗanda Korona ta kashe ba a yi musu rigakafin cutar ba.
” Hanya ɗaya ce dai, kuma ita ce a yi rigakafi, waɗanda suka yi za su samu kariya, waɗanda basu yi ba sune ke cikin mummunar haɗari.
Waɗannan na daga cikin kalaman minista Osagie a cikin jawabin da yayi a wajen kaddamar da yina rigakafin Korona a jihar Edo.
Shugaban hukumar Cibiyoyin kiwon lafiya na kasa, Faisal Shuaib ya yi karin haske cewa cikin mutum miliyan 4,680,000 da aka yi wa rigakafin, mutum 1,865,127 sun yi rigakafin sau biyu, wato cikakke.
” Ina so in yo amfani da wannan dama domin yin kira a gare ku da ku rika horan mutane da su garzaya inda ake yin rigakafin a yi musu domin gwamnati ta aika da maganin wuraren da ake yin rigakafin.
A na shi jawabin gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya bayyana cewa an yi wa mutum sama da 130,000 rigakafin korona a jihar.
Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar,
Osaigbovo Iyokha wanda shine ya wakilci gwamnan a wajen taron ya ce burin gwamnati shine ta iya yi wa akalla kashi 60 cikin 100 na mutanen jihar.
Discussion about this post