Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rajista ta Ƙasa, wato Corporate Affairs Commission (CAC), ta kammala yi wa Hukumar NNPC rajista daga hukuma, inda yanzu ya koma kamfani tantagarya.
An yi masa rajistar sauya fasali zuwa kamfani kamar yadda sabuwar dokar fetur ta PIA ta tsara, wadda Buhari ya sa wa hannu a ranar 16 Ga Agusta, 2021.
Sashe na 53(1) na sabuwar dokar ta PIA na buƙatar a tabbatar Ministan Harkokin Fetur tare da Ministar Harkokin Kuɗaɗe sun yi wa NNPC rajista, kafin cikar watanni shida da kafa sabuwar dokar.
Shugaban Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rajista, Garba Abubakar ne ya tabbatar da haka a Abuja, lokacin da ya ke taron ganawa da shugabannin hukumomi a Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Jari ta Ƙasa.
Ya ƙara da cewa an yi wa NNPC rajista kuma an kammala duk a rana ɗaya, saboda kamfanin ya cika dukkan sharuɗɗan da CAC ta gindiya kafin ya zama Ltd.
Batun ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi don yi wa ƙananan kamfanoni 250, 000 rajista, ya ce aikin na nan, kawai dai ana jiran cikon guda 3,000 ne kacal.
Ya ƙara da cewa ya na da yaƙinin nan da ƙarshen makon farko na watan Oktoba za a kammala komai.
Sauran waɗanda su ka yi jawabai a wurin sun haɗa da Ministan Kasuwanci da Zuba Jari, Niyi Adebayo, Ƙaramar Minista Maryam Katagum.
Discussion about this post