Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa sabuwar ƙwandalar ‘dijital’ ta e-Naira da za a fito da ita, zai kasance wani kuɗin Hada-hadar da za a riƙa amfani da shi baya ga Naira, kamar yadda dokar ƙasa ta amince da shi.
Babban Bankin Najeriya ne ya bayyana haka ta bakin Daraktan Tsare-tsaren Biyan Kuɗaɗe na CBN, Musa Jimoh ya bayyana a ranar Litinin.
Ya yi wannan ƙarin haske ne a lokacin da gidan talabijin na Channels ke tattaunawa da shi a ranar Litinin.
“A yau duk inda ka miƙa naira tilas a karɓa a matsayin ta na takardar kuɗin da dokar Najeriya ta amince a yi hada-hada da ita. To haka abin ya ke da wannan sabuwar ƙwandalar e-Naira da za a fito da ita a ranar 1 Ga Oktoba, 2021. Duk wanda aka bai wa e-Naira tilas ya karɓa.” Inji Jimoh.
A ranar 30 Ga Agusta ne CBN ya bayyana fito da e-Naira daga ranar 1 Ga Oktoba.
Za a fito da ita ce domin ta maye gurbin ‘cryptocurrency’ a ƙasar nan, bayan da CBN ɗin ya haramta, tun a cikin watan Fabrairu.
E-Naira dai ba wasu ƙwandaloli ne za a riƙa yawo da su a cikin aljihu ba. Hada-hadar kuɗaɗe ce ta intanet.
Dalili kenan ma CBN ya yi kira ga duk mai wayar sadarwa samfurin Android ko iPhone cewa su kwashi manhajar e-Naira wallet a daga rumbun kwasar manhajojin ‘application stores’ a wayoyin su.
Da aka tambaye shi anya Najeriya ta shirya bin wannan tsari kuwa, domin ana ganin za a iya fuskantar matsaloli a tsarin hada-hadar e-Naira.
Amma sai ya ce ba ya tsammanin wannan tsari ya na da wahalar da zai iya kawo wani cikas ko matsala a ƙasar nan.
“Ai ba cewa aka yi rana ɗaya kowa tilas ya karɓe ta ba, ko ya yi mu’amala da ita ba. Abin zai ɗan ɗauki lokaci, kafin ya karaɗe ko’ina na sassan ƙasar nan da kuma kowane irin hada-hadar kasuwanci.”
“Idan ka tuna a baya akwai lokacin da a ƙasar nan ba kowa ke yarda da tsarin POS ba. Amma yanzu kuma ya cika ko’ina.”
A ƙarshe ya wani ƙarin alfanun e-Naira shi ne za a rage buga takardun kuɗaɗe, kuma za a rage yawan jigilar kuɗaɗe daga nan zuwa can.
Discussion about this post