Majalisar Dattawa ta aika wa Buhari saƙon gaggawa cewa ya fito ya gaggauta raɗa wa ‘yan bindiga suna ‘yan bindiga, kuma ya bada ƙaƙƙarfan umarnin kakkaɓe su baki ɗaya a huta.
Sannan kuma sun buƙaci Buhari ya yi shelar neman kwamandojin ‘yan bindiga ruwa-jallo, ko da rai ko babu. Sun ce a gaggauta zaƙulo duk inda su ke domin a kama su a hukunta su daidai da laifin ta’addancin da su ke yi.
“A Sa Bam A Dagargaje Su Kawai” -Majalisar Dattawa:
Haka kuma Majalisar Dattawa ta nemi Buhari ya bada umarni “a sa bama-bamai a dagargaje su kawai a dukkan sansanonin da su ke a ɓoye.
Waɗannan na kaɗan daga cikin buƙatun da Zauren Majalisar Dattawa ta amince da su a kan ta’addancin ‘yan bindiga, muradun da Sanata Ibrahim Gobir ya gabatar a ranar Laraba.
Sanata Gobir na wakiltar Shiyyar Sokoto ta Gabas, a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Koken sa ya zo kwana ɗaya bayan ‘yan bindiga sun kutsa cikin Garin Gatawa a Karamar Hukumar Sabon Birni, sun kashe aƙalla mutum 20, sun yi garkuwa da wasu da dama. Sabon Birni na cikin Jihar Sokoto.
Haka kuma kwana ɗaya kafin harin Gatawa, ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a ƙauyen Gangara, duk a cikin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ɗin.
Gobir ya ce a yanzu shiyyar Sokoto ta Gabas ta zama ‘Daular ‘Yan Bindiga’, saboda sun yi kaka-gida can, bayan guje wa ruwan wutar da sojoji ke masu a Zamfara.
Daga nan sai ya yi misalai da hare-haren da su ka kai a Gatawa da Gangara a ranar Talata.
“Asarar sojojin da ake yi a hannun ‘yan bindiga zai iya rage ƙarfin yawan sojojin da ake da su, sannan kuma hakan zai ƙara kawo ƙarin taɓarɓarewar tsaro a ƙasar nan.
“Yawancin ‘yan bindigar Zamfara sun arce zuwa ƙananan Hukumomin Sabon Birni da Isa a Jihar Sokoto.”
Ya yi ƙorafin cewa hare-haren da ake kai wa ‘yan bindiga a Zamfara kaɗai ya ke tasiri, banda sauran jihohi.
Wata Sanata ‘yar PDP daga Jihar Anambra, mai suna Uche Ekwunife, ta ce kada hankalin batun tsaro ya fi maida hankali a Kudu maso Gabas kaɗai.
Ta ce kamata ya yi Shugaba Buhari ya fito ya yi wa ƙasar nan jawabi. “Saboda shirin da ya yi abin damuwa ne matuƙa.”
Discussion about this post