RASHIN TSARO: Sojojin Najeriya sun halaka dakarun ta’addancin ISWAP shida, sun ƙwato makamai

0

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana samun nasarar bindige ‘yan ta’addar ISWAP shida tare da ƙwato manyan makamai, a wani gumurzun ɓarin-wuta da su ka yi.

Kakakin Sojojin Najeriya Onyema Nwachukwu ne ya sanar da haka, cikin wata sanarwar da ya fitar a Abuja, a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ƙara da cewa an kashe Boko Haram ɗin ne a gumurzun yaƙi biyu a aka gwamza daban-daban da su.

“Dakarun Birged ta 25 da ke ƙarƙashin Operation Haɗin Kai ne su ka kashe Boko Haram huɗu a ranar 31 Ga Agusta, 2021.

“Sai kuma wasu ‘yan ta’adda masu hare-haren sari-ka-noƙe a tsakanin Damboa-Bulabulin-Maiduguri, su ma su ka gamu da gamon su, inda sojojin Najeriya su ka gama da su.

“Baya ga wannan kuma Sojojin Najeriya sun ƙwato AK47 huɗu, sai kuma jigidar albarusai” Inji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara dacewa sojojin Bataliya ta 195 sun kashe wasu ‘yan ta’adda biyu, a inda su ke sintiri tare da CJTF a Garejin Dusman-Muna.

Wannan nasara na samuwa a daidai lokacin da dubban ‘yan ta’adda ke ƙara miƙa wuya, kuma jama’a ke kaffa-kaffa da karɓar tubar su.

Premium Times ta buga labarin yadda Dattawan Barno sun karɓi ƙaddarar zama da tubabbun ‘yan Boko Haram 3,00.

Sun kashe dubbai, babu diyya. Sun maida rayuwar miliyoyin jama’a a sansanonin gudun hijira. Sun kashe dubban jami’an tsaro. Sun maida matan wasu da ‘ya’yan wasu matayen su, duk babu hukunci. Daga baya Gwamnatin Tarayya ta yi sun tuba, ta yafe wa ‘yan Boko Haram 3,000 kuma an roƙi al’ummar da waɗannan tubabbun ‘yan ta’adda su ka kassara cewa su karɓe su, su ci gaba da rayuwa a cikin su.

Haka wannan al’amari ya faru ranar Lahadi a Jihar Barno, inda bayan an yi ja-in-ja, daga baya shugabannin al’umma a jihar su ka amince da roƙon da gwamnati ta yi masu cewa su amince tubabbun ‘yan Boko Haram 3,000 su dawo cikin su, a ci gaba da rayuwa tare.

An ɗauki wannan mataki ne a wani taron masu ruwa da tsaki domin ganin an kawo ƙarshen gagarumar matsalar tsaro a Jihar Barno.

Taron dai Gwamnatin Jihar Barno ta shirya shi, bayan Gwamnatin Tarayya ta yafe wa ‘yan Boko Haram ɗin, kuma an gama yi masu huɗubobi, nasihohi da wankin ƙwaƙwalwar kankare masu aƙidar ta’addanci a ƙwaƙwalen su, abin da gwamnatin tarayya ke kira a Turance da ‘de-radicalization’.

Gwamnatin Jihar Barno ta bayyana cewa aƙalla akwai ‘yan ta’adda 3,000 da su ka ajiye makamai su ka yi saranda ga sojojin Najeriya.

Gwamna Babagana Zulum da ya shugabanci taron, ya bayyana cewa baya ga 3,000 ɗin da su ka yi saranda ga sojojin Najeriya, akwai ma wasu ‘yan Boko Haram ɗin su 900 da su ka yi saranda ga sojojin Kamaru.

Zulum ya ce taron mafitar ya zama tilas ganin yadda dubban ‘yan Boko Haram ke ta tururuwar miƙa wuya.

Shugabannin yankunan jama’a daban-daban sun bayar da shawarwarin yadda za a bi matakan da za a karɓi ‘yan ta’addar bayan an sake su.

An shafe sama da sa’o’i biyar ana tattaunawa, inda a ƙarshe aka fitar da tsare-tsaren sharuɗɗan sake karɓar su cikin al’umma.

Taron dai ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin addinai, masu riƙe da sarautun gargajiya, jami’an tsaro da kungiyoyi daban-daban.

Waɗanda su ka yi jawabai sun haɗa da ‘yan Majalisar Tarayya, na Jiha, sojoji da sauran wakilan jami’an tsaro.

Sauran waɗanda su ka yi magana sun haɗa da waɗanda Boko Haram su ka kassara rayuwar su ko ta ‘yan uwan su da wakilan Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya.

Sharuɗɗa da shawarwarin da su ka ɗauka dai Kwamishinan Shari’a na Jihar Barno Kaka-Shehu Lawan ne ya sa masu hannu.

Sun nemi Gwamnantin Tarayya ta ɗauki batun tubar ‘yan Boko Haram da kaffa-kaffa, kuma bisa matakan da doka ta tanadar.

Share.

game da Author