Sarkin Borgu da ke cikin Jihar Neja, Muhammad Ɗantoro ya roƙi Shugaba Muhammadu Buhari ya jibge sojoji a masarautar sa domin su magance matsalar tsaro a yankin sa.
Sarkin ya yi wannan kira ne kwana ɗaya bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Hakimin Wawa, Mahmoud Ahmed a ranar Asabar.
Ya ce kiran ya zama wajibi, domin su na bakin Dajin Borgu, inda Kainji ya ke.
Basaraken ya kuma ƙaryata raɗe-raɗin da aka riƙa yaɗawa cewa wai shi ma an yi garkuwa da shi. Ya ce ya na nan lafiya ƙalau, ba a sace shi ba.
“Ina ta samun kiraye-kirayen waya daga jama’a na kusa da na nesa, masu so su ji shin da gaske an yi garkuwa da ni?”
Sarkin ya ce ba shi ne aka yi garkuwa da shi ba. Hakimin Wawa ne aka yi garkuwa da shi.
“Sannan kuma an yi garkuwa da Hakimin Dekara kusan watanni huɗu kenan, har yau ba a same shi ko sake shi ba.
“Lamarin ya tayar min hankali matuƙa. Shi ya sa na ke roƙon a turo sojoji domin su zo su kutsa cikin Dajin Kainji su ƙwato mana hakiman da ke hannun ‘yan bindiga a cikin wannan wawakeken daji.”
Ya yi roƙon a gaggauta kai masu sojoji, tun kafin ‘yan bindiga su nausa cikin kan iyakokin Jamhuriyar Benin.
A ranar Lahadi wannan jarida ta bada labarin yadda mahara sun yi gaba da Hakimi a Masarautar Borgu.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja sun tabbatar da labarin yin garkuwa da Hakimin Wawa da ke cikin Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.
Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadi cewa an arce da hakimin wajen ƙarfe 10 na dare a ranar Azabar.
Sai dai kuma ya ce zaratan ‘yan sanda tare da ‘yan bijilante sun afka daji domin ƙoƙarin ceto hakimin.
Yayin da ya bada tabbacin ganin cewa za su yi bakin ƙoƙarin ganin an ceto hakimin, Abiodun ya kuma roƙi jama’a su riƙa kwarmata wa jami’an tsaro duk inda su ka ji motsin wani mugu da inda duk su ka san mugaye na fakewa.
Jihar Neja na ɗaya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga su ka yi wa kakagida.
Ta na daga cikin jihohin da gwamnonin su su ka haramta cin kasuwannin mako-mako a cikin wannan mako.