• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Buhari Travelling

    Duk da tsananin hare-haren da ya darkaki Najeriya a kwanakin nan Buhari zai waske taro Dakar

    An cika sansani uku fal da tubabbun ‘yan Boko Haram -Gwamna Zulum

    RUƊANI A APC: Gwamnan Neja, Bello ya ɗare kujerar Buni, Buhari ya bada umarnin Buni ya sauka daga shugabancin jam’iyyar

    IHU BAYAN HARIN SHIRORO: Gwamnatin Neja ta dakatar da haƙar ma’adinai a Shiroro, Munya da Rafi

    Barayi sun lalata tiransifoma 20 cikin makonni uku – Kamfanin Raba Wutar Lantarki

    SADAKA GUZURIN KIYAMA: Tsohon gwamnan da ya taya akanta jidar naira biliyan 84, ya yi wa malamai da ‘yan APC watandar shanu 370, ragunan layya 3,500 a Zamfara

    ZAƁEN GWAMNAN ANAMBRA: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

    ZAƁEN GWAMNAN OSUN: Matsalar tsaro da guguwar sayen ƙuri’u ne abin da ya fi damun mu -INEC

    Ƴan sanda sun ceto ƙananan yara 50 da aka kulle cikin kurkukun wani coci a ƙarƙashin ƙasa, a Ondo

    ‘Na sadaukar da rayuwa ta ga Najeriya’ – Inji sojan da mahara su ka kashe a harin Shiroro

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    LMC ta ci tarar Kano Pillars, ta kori shugabanta, Jambul bayan ya gobza wa ‘Rafiri’ naushi a haɓa

    Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

No Result
View All Result

RAHOTO: INEC za ta magance matsalolin na’urar zaɓe kafin zaɓen Gwamnan Anambra da za a yi cikin Nuwamba – Farfesa Yakubu

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
September 16, 2021
in Rahotanni
0
Yawan hare-hare kan ofisoshin INEC zai iya kawo wa zabukan 2023 cikas -Farfesa Yakubu

A ƙoƙarin ta na samar da sahihin zaɓe, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta tunkari matsalolin da aka fuskanta da sabuwar na’urar kimiyyar zamani da ake tantance masu zaɓe da ita, mai suna ‘Bimodal Voter Accreditation System’ (BVAS), a lokacin zaɓen cike gurbi da aka yi a Mazaɓar Jiha ta  Isoko ta Kudu 1 da ke Jihar Delta a ranar Asabar da ta gabata.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron da hukumar ta yi don rantsar sababbin manyan kwamishinoni uku da Kwamishinan Zaɓe Razdan (REC) guda ɗaya a Abuja a ranar Laraba.

Yakubu ya ce a yayin da aka ji daɗin sakamakon aikin da na’urar ta yi a rumfunan zaɓe 84 a lokacin zaɓen, an kuma ci karo da wasu ‘yan ƙalubale waɗanda za a magance su kafin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da za a yi a ranar 6 ga Nuwamba.

Yakubu ya tuno da cewa INEC ta kafa tarihi a ranar 8 ga Agusta lokacin da ta samu babbar nasarar gudanar da zaɓen farko a lokacin zaman annobar korona a zaɓen cike gurbi na Mazaɓar Jiha ta Nasarawa ta Tsakiya.

Ya tuno da cewa a wancan zaɓen, a karon farko INEC ta kuma riƙa tura sakamakon zaɓe kai-tsaye ta hanyar intanet daga cibiyoyin zaɓe zuwa gidan yanar da ake duba sakamakon zaɓe na INEC, wato ‘Result Viewing Portal’ (IReV).

Ya ƙara da cewa daga wancan lokaci zuwa yanzu, an zuba sakamakon wasu zaɓuɓɓukan har 26 a gidan yanar.

Ya ce, “Ko a ƙarshen makon nan da ya gabata, mun ƙara yin amfani da wata sabuwar fasaha a zaɓen cike gurbi na mazaɓar Isoko ta Kudu 1 a Delta.

“Mun shigo da na’urar BVAS don samun ingancin aikin tantance mutane ta hanyar ɗaukar bayanan mutum da ke aje a komfuta, inda aka yi amfani da taswirar yatsa da gane fuskar mutane masu zaɓe.

“Sakamakon da aka samu daga aikin farko da aka yi a cibiyoyin zaɓe 84 ya bada ƙwarin gwiwa sosai. A cikin misalin minti ɗaya kacal na’urar ta ke gano mai zaɓe a cikin komfuta sannan cikin wasu mintinan biyu ta ke tantance mai zaɓe.

“Ta ɓangaren nagartar na’urar da ƙarfin batirin ta kuwa, babu na’urar BVAS ko ɗaya da aka maye gurbin ta da wata a dalilin mutuwar batiri a duk tsawon lokacin zaɓen.

“Abu mafi muhimmanci shi ne, na’urar ta samar da tabbacin tantance mai zaɓe ta hanyar hana mutum ya kaɗa ƙuri’a sama da sau ɗaya ko ya yi amfani da katin zaɓe na sata.

“Dukkan masu zaɓe an tantance su ta hanyar na’urar BVAS. Don haka an magance yin aiki da fom ɗin kai kuka. Zaɓen cike gurbi na mazaɓar jiha ta Isoko ta Kudu 1 ya zama abin tarihi ta wannan fuskar.”

Shugaban na INEC ya ce to amma akwai wasu ‘yan mishkiloli da aka samu dangane da na’urorin kimiyya a lokacin zaɓen. Waɗannan matsaloli, a cewar sa, sun haɗa da wahalar da ake fuskanta wajen yadda na’urar BVAS ta ke tabbatar da hoton mutum da ke zaune a gaban ta da wanda aka ɗora a kan rajista a wasu ‘yan lokuta,   saboda rashin kyan hotunan wasu masu zaɓe wanda hakan ya faru ne daga rajistar baya da aka yi.

Ya ce, “Na biyu, babu haske sosai a wasu cibiyoyin zaɓen a lokacin da ake ɗaukar hoton fuska don tantancewa.

“Na uku, akwai daɗaɗɗiyar matsalar nan ta shigowar ‘yan daba a lokacin zaɓe. An kai wa ma’aikatan mu hari inda ‘yan daba su ka ƙwace na’urorin BVAS guda biyar.

“Duk da yake wannan bai shafi gudanar da zaɓen ba saboda mun tura ƙarin na’urori da aka aje a matsayin shirin ko-ta-kwana, ‘yan sanda na binciken faruwar al’amarin.

“Duk da haka, mu na so mu tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa hukumar mu za ta magance waɗannan matsalolin, ciki har da sanya wata manhaja da za ta iya hana na’urar da aka sace yin aiki kuma ta gano ta.

“Za a fara aiki da wannan manhajar daga yanzu zuwa lokacin zaɓen gwamnan Anambra da ke tafe.”

A kan batun zaɓen gwamnan Anambra da za a yi a ranar 6 ga Nuwamba, Yakubu ya ce an yi nisa wajen shirye-shiryen zaɓen domin har ma an aiwatar da abubuwa masu yawa a cikin tsare-tsare da jadawalin al’amuran zaɓen.

Ya ce niyyar INEC ita ce ta ci gaba da gyara ingancin tsarin zaɓe ta hanyar haɓaka duk wani tsari da aka yi, da gudanarwa, aiwatarwa da kuma hanyoyin tallafi ta hanyar yin amfani da kimiyyar da ta dace.

Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa sababbin manyan kwamishinonin zaɓe da INEC ta yi wa marhabin su ne Farfesa Abdullahi Zuru, wanda tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Kebbi da Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ne; da Farfesa Sani Adam, wanda lauya ne kuma Muƙaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar Abuja ne, da kuma Dakta Baba Bila, wanda akanta ne kuma tsohon Ma’ajin Jami’ar Benin.

NAN ta ruwaito cewa sabon kwamishinan zaɓen (REC) da aka rantsar shi ne Farfesa Sa’idu Ahmad, wanda Farfesan Adabin Ingilishi ne daga Jami’ar Bayero, Kano.

Ahmad, wanda an tura shi Jihar Zamfara domin kama aiki, ya cike gurbin Jigawa wadda ta kasance ita kaɗai ce jihar da ba ta da kwamishina (REC) a hukumar, bayan ƙarewar wa’adin Abdullahi Kaugama, wanda ya yi aiki a matsayin Sakataren hukumar.

A yayin da Yakubu ya ke yi wa sababbin kwamishinonin zaɓen su uku da kuma sabon REC ɗin maraba, ya yi kira a gare su da su taimaka wajen ɗaga martabar hukumar wajen gudanar da zaɓuɓɓuka nagartattu a ƙasar nan.

Ya ce, “Aikin da ke gaban mu mai wahala ne, to amma kuma aiki ne na bauta wa ƙasa. Ya na da muhimmanci ku zauna ku yi karatun ta-natsu don ku fahimci ƙa’idoji, hanyoyi da nauyin ofis ɗin ku.

“Bari in ƙara nanata cewa ku saka a ran ku a ko yaushe cewa samun ingantaccen zaɓe ya dogara a kan samun ingantattun masu gudanar da zaɓen. Ina kira a gare ku da ku kama mana wajen ƙara ɗaga martabar mu.”

Ya bayyana tabbacin cewa waɗannan mutum huɗu da aka naɗa za su kawo wa hukumar tarin ilimin su da masaniyar su a matsayin su na malamai kuma masu gudanarwa, wajen ƙara faɗaɗa iyakokin yin zaɓe mai inganci a Nijeriya.

Yakubu ya shawarce su da su riƙe martabar INEC kuma su bi ƙa’idoji da dokoki sau da ƙafa wajen aiwatar da aikin da ya rataya a wuyan su.

Ya ce, “Bayan mun dage wajen bin tanade-tanaden doka, nasarar mu a wannan mawuyacin aiki kuma ya dogara ne ga namu mutuncin a matsayin manajojin zaɓe.

“Tilas mu tsaya ƙyam wajen aiki da doka, mu tsaya ƙyam wajen riƙe amanar jama’a da ke kan mu, kuma mu yi adalci wajen mu’amalar mu da jam’iyyun siyasa da kuma ‘yan takara.

“Tilas mu tuna cewa a wajen sauke nauyin da ke kan mu, dole ne mu sa Nijeriya da ‘yan Nijeriya a sahun farko.

“Tilas mu yi aiki da rantsuwar kama aiki da mu ka yi don kare zaɓin da ‘yan Nijeriya su ka yi wa kan su a dukkan zaɓe, kuma mu ci gaba da kare darajar zaɓe wanda idan babu shi to zaɓen dimokiraɗiyya bai da wata ma’ana.”

A lokacin da ya ke jawabi a madadin sauran waɗanda aka naɗa ɗin, Farfesa Zuru ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin Majalisar Tarayya saboda zaɓo su da aka yi aka ga sun dace a ba su wannan muhimmin aiki na bauta wa ƙasa.

Zuru ya sha alwashin za su yi aiki da rantsuwar su ta kama aiki tare da tsare gaskiya kuma ba tare da jin tsoro ko nuna bambanci ba wajen gudanar da aikin su.

Ya ƙara da cewa tare da jagorancin Farfesa Yakubu, su da aka naɗa za su sanya INEC da ‘yan Nijeriya su yi alfahari wajen ciyar da ruhin dimokiraɗiyya gaba a Nijeriya.

Ya ce, “Ina so in tabbatar da wa ‘yan Nijeriya cewa burin mu shi ne mu gudanar da zaɓe fisabilillahi a kowane mataki.

“Wannan shi ne tabbacin da mu ke ba dukkan ‘yan Nijeriya da kuma Ubangijin mu.”

Tags: AbujaHausaHukumar ZaɓeLabaraiNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

FARGABAR GARKUWA DA ƊALIBAI: Fiye da yara miliyan 1 na tsoron komawa makaranta a Arewa -UNICEF

Next Post

IDAN DAMBU YA YI YAWA: ‘Za a ƙara narka maƙudan kuɗaɗe a gina gadoji da ƙananan titina a babban titin Legas zuwa Ibadan’ – Fashola

IDAN DAMBU YA YI YAWA: 'Za a ƙara narka maƙudan kuɗaɗe a gina gadoji da ƙananan titina a babban titin Legas zuwa Ibadan' - Fashola

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • KOWA TA SA TA FISSHE SHI: Ƙoƙarin haɗewar LP da NNPP ya kakare, Peter Obi zai bayyana mataimakin takarar sa ranar Juma’a
  • ‘Da gangar aka bari ƴan bindiga suka kai harin gidan yarin Kuje, saboda na yi ta faɗin hakan zai auku – Mamu
  • Ƴan bindiga sun babbake cibiyoyin kiwon lafiya sun yi dalilin dole aka rufe wasu 69 a Katsina
  • Dala ta ƙara kekketa wa naira rigar mutunci daidai lokacin tsadar kayan abinci
  • Duk da tsananin hare-haren da ya darkaki Najeriya a kwanakin nan Buhari zai waske taro Dakar

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.