A yau Talata ce manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa biyu da su ka fi sauran ƙungiyoyi tara ‘yan wasa masu tsada za su kece-raini, a gasar cin Kofin Champions League na Turai.
PSG ta Faransa za ta kara da Manchester City ta Ingila, a filin wasa mai alfarma da martaba na Parc des Princes da ke Paris.
Ƙungiyoyin biyu mashahuran attajiran Larabawa ne su ka mallake su, kuma sun fi sauran ƙungiyoyi yawan ‘yan wasa masu tsada.
An ƙiyasta darajar ‘yan wasan PSG za su kai Euro miliyan 997.25 Su kuma na Manchester City za su kai Euro biliyan 1.005.
Gaba ɗayan su jimlar adadin darajar tsadar ‘yan wasan su ta haura Euro biliyan 2. Shi kuma kuɗin Euro ya fi Dalar Amurka daraja. Ita kuma Dalar Amurka ɗaya a kasuwar ‘yan canji, ta kai Naira 570.
Manchester City ta yi cinikin ɗan wasa ɗaya a wannan kakar cinikin ‘yan ƙwallo, wato Jack Grealish a kan Euro miliyan 117.5
Ita kuma PSG ta yi cinikin mashahuran ‘yan wasa a bana, irin su Achraf Hakimi, Sergio Ramos, Gianluigi Donnaruma da kuma tauraron duniya Leonel Messi.
Tsada ko darajar hatsabiban ‘yan gaban PSG masu maitar saka ƙwallo su uku wato Kylian Mbape, Nymar da Leonel Messi ta kai Euro miliyan 340.
Yayin da darajar Mbape ta kai Euro miliyan 160, Nymar ya kai Euro miliyan 100, shi kuma Messi Euro miliyan 80.
A Manchester City kuma Kevin de Bruyne ya kai darajar Euro miliyan 100. Raheem Sterling ya kai darajar Euro miliyan 90, shi kuma Phil Foden ya kai Euro miliyan 80.
Gaba ɗaya su ukun darajar su a kasuwar ƙwallon duniya ta kai Euro miliyan 270.
Yau fa ƙwallon masu kuɗi ce. Domin darajar ‘yan wasan ƙungiyon biyu ta haura naira tiriliyan ɗaya.
Ko PSG Za Ta Fara Huce Haushin Dukan Da Man City Ta Riƙa Yi Mata A Baya?:
Kafin haɗuwar yau dai ƙungiyoyin biyu sun taɓa kafsawa sau 5. Manchester City ta yi nasara kan PSG sau uku, an yi kunne-doki sau 2. PSG ba ta taɓa yin nasara kan Manchester City ko sau ɗaya ba.
Amma a yau a bisa dukkan alamu manyan malamai da masana da ‘yan duban ƙwallon ƙafa na ganin cewa yau magoya bayan PSG za su koma gida cikin annashuwa.