NNPC A HANNUN ‘YAN WALA-WALA: Yadda aka sayar da gurɓataccen mai na biliyoyin nairori ga kamfanin bogi

0

Wannan wani bincike ne na musamman da PREMIUM TIMES ta bankaɗo wata harƙalla da cuwa-cuwar da aka binne kwanan nan a NNPC.

Mai karatu zai fi gane yadda aka yi wala-wala da harƙalla, idan aka yi masa dalla-dalla, kamar yadda zai karanta a ƙasa:

Yaya Lamarin Ya Ke Ne?:

1. Shekaru biyu da su ka gabata, an dakatar da aikin tace ɗanyen mai a matatun Fatakwal, Warri da Kaduna, aka ce za a shafe watanni 44 ana gyare-gyare.

2. Ƙarancin kuɗaɗe ya damu NNPC sai kamfanin ya yi tunanin kwashe dagwalon gurɓataccen ɗanyen mai da ake kira ‘Slop Oil’ domin a sayar, saboda wasu dalilai.

3. An yanke shawarar a sayar da ‘slop oil’ ga masana’antun cikin gida domin su riƙa amfani da shi wajen tayar da janareto, saboda ƙarancin gas.

4. Masana’antun sun fuskanci barazanar rashin wuta da ƙarancin gas, sai gwamnati ta ji tsoron kada su kwashe kayan su su koma ƙasashen da ke maƙautaka da Najeriya.

5. Dalili kenan ake sayar masu da gurɓataccen ɗanyen mai wato ‘slop oil’, domin sun riƙa tayar da janareto da shi su na sarrafa kayayyaki aka masana’antun.

6. Mene Ne ‘Slop Oil’?: ‘Slop Oil’ dai wani gurɓataccen ɗanyen mai ne, amma mai amfani. A NNPC ana kiran sa LPFO.

Ɗanyen mai ne wanda ake kwasowa a ƙasan manyan tankunan jiragen ruwa masu jigilar mai. Sai dai kuma ɗanyen mai ba gangariya ba ne. Ana samun sa ya gauraya da ruwa da kuma dabza-dabzar ɗanyen mai.

Akasari ana tara shi ne a duk lokacin da ake wanke manyan tankunan jiragen ruwan dakon danyen mai ko rumbunan tara ɗanyen mai.

7. Gada-gadar Yadda Aka Sayar Da Ɗanyen Man ‘Slop Oil’: An buga tandar neman kamfanonin mai masu buƙatar saye, kuma kamfanoni 18 su ka nemi a sayar masu. Kowanen su ya aika da farashin da zai iya sayen kowace lita.

8. Gurɓataccen man na ‘slop oil’ ɗin dai mai yawa ne, domin ya kai lita miliyan 30.

9. NNPC ta yi fatali da sauran tandar farashin kamfanoni 15, ta zaɓi kamfanoni 3 kacal, ta ce a cikin su za a sayar wa mai rabo.

10. Kamfanonin da NNPC ya zaɓa su ne:

*Sign Oil & Gas Ltd.
*Synthesis Integrated Pure Oil.
*Kurpo Energy Oil and Gas Ltd.

11. Yadda Lamarin Ya Rikiɗe Cuwa-cuwa Da Gada-gada:

PREMIUM TIMES ta bankaɗo cewa:

12. Waɗanda ke da Sign Oil & Gas Ltd, su ne dai ke da Synthesis Integrated Pure Oil & Gas Ltd.

13. Da PREMIUM TIMES ta matsa bincike a Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rajista (CAC), ta gano cewa Kurpo Energy ba shi da rajista a duniya ko a lahira. Babu wanda ya san ko na su wane ne.

14. Wani mai suna Orereh Kingsley da Orereh Oghenetejiri ne Daraktocin Sign Oil & Gas Ltd, kuma su dai ne Daraktocin Synthesis Integrated Pure Oil and Gas Ltd.

15. PREMIUM TIMES ta bankaɗo cewa akwai haɗin-baki tsakanin wasu manyan jami’an NNPC da kuma masu kamfanonin uku da aka zaɓa. Domin kusan su ukun duk farashi kusan ɗaya su ka buga tandar sayen kowace lita ɗaya ta ‘slop oil’.

15. Synthesis Integrated Pure Oil and Gas Ltd ya taya kowace lita 1 Naira 105. Shi kuma Sign Oil and Gas Ltd ya taya Naira 111. Yayin da Kurpo Energy Oil and Gas Ltd ya taya Naira 99.

17. PREMIUM TIMES ta gano cewa manyan jami’an NNPC sun san Kurpo Energy Oil and Gas Ltd ba shi da rajista a CAC. Ko kuma idon su ya rufe da cuwa-cuwa, ba su bi diddgin ko ya na da rajista ko babu ba, kamar yadda PREMIUM TIMES ta bi diddigi.

18. Wane Ne Uban Gada-gadar Buga Tandar Sayar Da Gurɓataccen ‘Slop Oil’?:

An buga wannan tanda tare da tantance kamfanoni uku a ƙarƙashin Babban Daraktan Kula Da Matatun Mai na Ƙasa, Mustapha Yakubu.

19. Kuma kamfanoni da masana’antu na cikin gida ya kamata a sayar wa ɗanyen man, domin a riƙa amfani da shi wajen tayar da janareto manya-manya da su ke amfani da shi.

Maimakon haka, sai aka sayar wa kamfanin bogi, wanda shi kuma ya sayar da man a waje, ba a cikin Najeriya ba.

20. Ɗanyen man da aka yi wa wannan gagarimar gada-gada a Matatar Fatakwal ya ke baki ɗayan sa.

21. Duniyar ‘Yan Wala-walar Ma’aikatan NNPC: A tarihin NNPC ba a taɓa sayar da ɗanyen gurɓataccen mai (‘slop oil’) a ƙasar waje ba, sai a wannan karo.

22. Wannan cinikin cikin duhu da harƙalla zai maida hannun agogo baya ga ƙoƙarin da Gwamnatin Buhari ke yi wajen ganin ta farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya.

23. Rufa-rufar Sayar Wa Kurpo Energy Oil and Gas ‘Slop Oil’: An bai wa Sign Oil and Gas Ltd wa’adin kwanaki 10 a ranar 22 Ga Yuni ya biya kuɗi, amma har zuwa ranar 7 Ga Yuli kuɗin ba su haɗu ba.

24. An soke gwangilar sayar da man aka bai wa Synthesis Integrated Pure Oil and Gas Ltd, a ranar 8 Ga Yuli, shi ma aka ba shi kwanaki 10 ya biya kuɗi. Amma har wa’adin kwanaki 10 su ka cika bai haɗa kuɗaɗen ba.

25. Daga nan sai aka damƙa wa kamfanin Kurpo Energy Oil and Gas Ltd, kamfanin da babu mai shi, ba shi da rajista a duniya ko a lahira.

26. PREMIUM TIMES ta yi ta buga lambar wayar kamfanin Kurpo, amma babu wanda aka samu, kuma lambar a kashe ta ke. Bisa dukkan alamu lambar ma ta bogi ce.

27. PREMIUM TIMES ta tuntuɓi NNPC dangane da wannan cuwa-cuwa, amma mahukuntan kamfanin su ka nemi wannan jarida ta ba su isasshen lokaci domin su yi bincike.

28. Wasu Kamfanonin Da Su Ka Nemi Cinikin Aka Hana Su:

Oando Energy
Yunusawa, Petroleum Resources Ltd,
North Bridge Energy Ltd,
SIK Oil and Gas Services Ltd.,
Gas Project Ltd.,
Speedo Energy Resources Ltd.,
PT Intim Perkasa,
AGM Musa Integrated,
Vigor Ltd.,
Imani Petroleum Company Ltd.,
A.Y Maikifi Oil & Gas.

Share.

game da Author