Nazarin Ganawar Gwamna Inuwa Yahaya Da Shugaba Buhari Da Kuma Muhimman Batutuwan Da Ya Baje Wa Buhari A Faifai

0

Ziyarar da Gwamna Muhami Inuwa Yahaya na Jihar Gwambe ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa, a Abuja, ta zama abin yabo da jinjina ga masu sharhin al’amurran yau da kullum da na siyasa.

Masu fashin baƙin ƙabli da ba’adin siyasa na ganin wannan ziyasa wani kadarko ne da Gwamna Inuwa Yahaya ya gina bisa nagartattun tubali da ginshiƙin ci gaban jiha, tun bayan hawan sa Gwamna shekaru biyu da su ka gabata.

Batutuwan da Gwamna ya tattauna tare da Shugaba Buhari sun kasance muhimmai ga batun tsaron ƙasar nan, ga inganta tattalin arziki, ƙara ƙulla danƙon zamantakewa a ƙasa da bunƙasa rayuwar al’umma.

Shin jama’a waɗanne batutuwa ne Gwamnan Jihar Gombe ya tattauna da Shugaban Ƙasa? Kuwa ta waɗanne hanyoyi ne waɗannan batutuwa za su zama alfanu ga Jihar Gombe da ƙasa baki ɗaya?

A wannan gaɓa dai ya kamata a sani cewa Gwamna Inuwa Yahaya ne da kan sa ya tsara batutuwan da ya bijirar ga Shugaba Buhari, waɗanda dukkan su batutuwa ne da za su zama alheri ga Jihar Gombe da al’ummar jihar baki ɗaya.

Na farko, Gwamna Inuwa Yahaya ya baje wa Buhari tafkekiyar taswirar tsarin Rukunin Masana’antun Gombe, wanda Gwamna da kan sa ya yi tunanin ginawa, kuma aka sa masa sunan Rukunin Masana’antun Muhammadu Buhari.

An ware fili mai faɗin kadada (hekta) 1,000 domin yin wannan katafaren aiki a cikin sa.

Kuma ana sa ran yin amfani da aikin makamashi na Daɗinkowa Hydro Power Plant domin ya riƙa samar da wuta ga rukunin masana’antun.

Gwamna Inuwa Yahaya: Aiki Ba Ya Sa Gaban Ka Ya Faɗi:

Tuni har Gwamnantin Jihar Gombe ta rattaba hannun amincewa za ta kashe fiye da naira biliyan 16.4 wajen kwangilar gina Rukunin Farko (phase 1) na aikin. Kuma tun da aka ƙirƙiro jihar Gombe cikin 1996, ba a taɓa bijiro da katafaren aiki kamar wannan ba a tarihin kafuwar jihar.

A ganawar da Gwamna Inuwa Yahaya ya yi tare da Wakilan Gidajen Jaridu a Fadar Shugaban Ƙasa, ya bayyana masu irin tattaunawar da ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari, ciki har da batun gina Rukuni ko Cibiyar Masana’antu da Kasuwanci, wadda aka raɗa wa sunan Muhammadu Buhari.

“Kun san mutanen mu manoma ne da kuma makiyaya. Saboda haka idan mu ka gina rukunin masana’antu, zai kasance mun samu babban wurin da zai ba mu damar matasan mu su samu tasiri a masana’antu, wajen ayyukan sarrafa kayan noma da kasuwancin sa da rarraba. Hakan kuma zai inganta rayuwar su tare da bunƙasa tattalin arziki.”

Gwamna Inuwa Yahaya da Shugaba Buhari sun tattauna a kan batutuwan tsaro, tare da yi masa bayanin irin kyakkyawar karɓa da tsugunar da ‘yan gudun hijira daga Barno, Yobe da Adamawa da Jihar Gombe ke yi.

Ya ce saboda zaman lafiyar da ake samu a Gombe, Jihar ta zama tundun-mun-tsira ga ɗimbin masu gudun hijira waɗanda Boko Haram su ka raba da muhallin su a Barno, Yobe da Adamawa.

Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna wa Shugaba Buhari irin kyawawan halin Gombawa wajen karɓar masu gudun hijira su na zama tare da su hannu bib-biyu.

Ya kuma tunantar kan yadda Jihar Gombe ta sadaukar da Sansanin Masu Bautar Ƙasa (NYSC Camp), inda ake yi wa tubabbun ‘yan Boko Haram horon kankare masu mummunar aƙidar ta’addanci a ƙwaƙwalen su.

A kan haka sai Gwamna Inuwa Yahaya ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta bai wa Gombe wasu kuɗaɗe domin ta gina wani sansanin NYSC ɗin badan.

Ya ce sake gina wani sansanin NYSC ya zama wajibi a Jihar Gombe, domin ganin yadda Boko Haram ke ta miƙa wuya ga sojoji, to ba a san ranar da za a daina jibge tubabbun ‘yan ta’adda a sansanin NYSC na Gombe da ake ajiye su a ciki ba a yanzu.

Haka kuma Gwamna Inuwa Yahaya ya gabatar wa Shugaba Buhari daftarin gandun makiyaya da za a gina a Wawa-Zange. Ya nuna masa muhimmancin gaggauta ginin wanda zai ƙunshi hekta 144,000.

Gwamnan tare da Shugaban Ƙasa sun tattauna batun fetur da gas da aka samu a zirin Benuwai Trough, musamman a yankin Kolmani, wanda ke cikin jihohin Gombe da Bauchi.

A wurin wannan ganawa dai Gwamna Inuwa Yahaya ya yi rawar-gani. Ya nuna cewa jagora ne shi nagari, sannan batutuwan da ya bijirar ga Shugaba Muhammadu Buhari, sun ƙara tabbatar da cewa Gombawa ba su yi zaɓen-tumun-dare ba.

Tabbas Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna wa Fadar Shugaban Ƙasa cewa shi riƙaƙƙen falke ne, wanda ya san inda ake zuwa a yi fatauci har a ci riba mai yawa, kuma mai albarka.

Ismail Uba Misilli ne Darekta Janar na harkokin da suka shafi yaɗa labarai daga fadar gwamnatin jihar Gombe.

Share.

game da Author