Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa Najeriya ta samu gagarimar nasarar daƙile ayyukan ta’addanci da kuma toshe hanyoyin da wasu masu hali ke bi su na ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda.
Da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a birnin New York, inda ake taron Shugabannin Duniya a Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya, Malami ya ƙara da cewa mahukuntan Najeriya sun samu nasarar gano masu ɗaukar nauyin ta’addanci a ƙasar kuma an damƙe su.
Ya ce wannan ya taimaka sosai wajen samun nasarar daƙile ayyukan ta’addanci sosai, musamman a Yankin Arewa maso Gabas.
Wannan bayani na sa ya zo daidai da lokacin da mahukuntan Sojojin Najeriya su ka bayyana cewa aƙalla akwai Boko Haram da iyalan su za su kai 8,000 da su ka yi saranda cikin ‘yan watannin nan.
Idan ba a manta ba, Malami ta bayyana a cikin watan Mayu cewa an samu nasarar kama mutum 400 da ake zargin su na ɗaukar nauyin Boko Haram, kuma za a fara shari’ar su a kotuna.
A New York, Malami ya ce “tsauraran matakan da gwamnatin Najeriya ke ɗauka sun kawo gagarimar nasarar daƙile ta’addanci da kuma toshe ƙofofin da wasu ke amfani da kuɗaɗe su na ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda.”
Sai dai kuma ministan ya ce a yanzu da ake kan matakin bincike da shari’a, ba za a bayyana sunayen su ba.
Kalamin sa ya yi daidai da na Femi Adesina, Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya ce Najeriya ba za ta fallasa masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’addar da UAE ta zarga da ɗaukar nauyin ta’addanci ba.
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Najeriya ba za ta fallasa masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda ba.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana haka a lokacin da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin na Channels, ranar Litinin a Abuja.
Adesina ya ce maimakon a fito ana fallasa su ko a kunyata ta su, gwamnati ta maida hankali ne wajen tabbatar da cewa an gurfanar da su, an hukunta su.
Adesina na magana ne a kan wasu ‘yan Najeriya shida da ƙasar UAE ta lissafa a cikin jerin mutum 38 da ta ce su na ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda.
“Najeriya ba za ta fallasa su ko ta kunyata su kowa ya gan su ya san su a yanzu ba. Maimakon haka, ta maida hankali ne a kan ganin an hukunta su.
“Kuma tun lokacin da UAE ta fito da bayanin, Ministan Shari’a na Najeriya ya yi magana ya ce za a gaggauta tuhumar su da yanke masu hukunci.
“Saboda haka mai yiwuwa yanzu bincike ya na matakin EFCC. Ko kuma ba mamaki ya na hannun Hukumar Leƙen Asiri ta NIA.” Inji Adesina.
Da aka taɓo masa batun shin ko Buhari zai sake kinkimo bashi a Taron Shugabannin Ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya, sai Adesina ya ce ai taron ba na neman bashi ba ne.
“Ba taron neman bashi ba ne. Amma dai wasu shugabannin kan keɓe su tattauna hulɗoɗi a tsakanin ƙasashen su. Kuma bashin da Shugaba Buhari ke ciwowa a yanzu ai ana yin ayyukan raya ƙasa ne da su. Saɓanin Gwamnatin baya, wadda idan an ciwo bashin, a cikin aljifan su su ke danna maƙudan kuɗaɗen.” Cewar Adesina.