Hukumar Binciken Hatsarin Jiragen Sama (AIB), ta damƙa rahoton binciken da ta kammala domin gano musabbabin hatsarin jirgin da ya kashe tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya, Janar Attahiru.
Janar Attahiru ya rasu a hatsarin wani jirgi a Kaduna, tare da wasu mutum 10, waɗanda biyar daga cikin su duk manyan hafsoshin sojojin Najeriya ne.
Bayan rasuwar ta su, an umarci Hukumar AIB, wato ‘Accident Intelligence Bureau’ ta gano musabbabin hatsarin.
Da ya ke miƙa rahoton ga Babban Hafsan Sojojin Sama, Isyaka Amao, Shugaban AIB Akin Olateru ya bayyana cewa sun gano wasu batutuwa 27 dangane da hatsarin jirgin, kuma akwai shawarwarin da masu binciken su ka bayar duk a cikin rahoton.
Ba a dai bayyana abin da ke cikin rahoton ba.
Idan ba a manta ta, ko a zamanin mulkin Goodluck Jonathan, wani hatsarin jirgi ya yi sanadiyyar mutuwar babban Hafsan Sojojin Najeriya a lokacin, Janar Andrew Azazi da kuma Gwamnan Jihar Kaduna na lokacin Patrick Yakowa.
Haka nan a zamanin mulkin Obasanjo, jirgin fasinjoji da ya tashi daga Abuja zuwa Sokoto, ya yi sanadiyyar mutuwar Sultan Abubakar Macciɗo da wasu manyan ƙasar nan da dama.
Discussion about this post