Kungiyar Iyayen Daliban Makarantar Islamiyya ta Tegina sun bayyana cewa sai da suka tara naira miliyan 8 suka aika wa ‘yan bindiga kafin aka sakar musu ƴaƴa.
Waɗannan sune kalaman da iyayen suka faɗi a wajen taron kungiyar iyayen makarantar da suka yi a garin Tegina ranar Lahadi bayan an sako musu ƴaƴa.
Shugaban kungiyar Abdullahi Sirajo ya bayyana cewa iya miliyan 8 suka iya haɗawa sai dai bai bayyana ko nawa ne adadin kuɗin da aka kai wa ƴan bindigan kafin su saki yaran Islamiyyar da suka sace.
Sai dai kuma da yawa daga cikin iyayen yaran da aka sako sun ce ba za su sake kyale ƴaƴan su su koma wannan makaranta ba saboda tsoron kada a sake dauke musu su, barci ya sake gagarar su.
Iyayen sun ce basu gamsu da tsaron da aka saka a makarantar ba.
Shugaban makarantar ya roki iyayen yaran su yi hakuri kada su cire ƴaƴan su daga makarantar yana mai cewa lallai hukumar makarantar da gwamnati na kokarin ganin abinda ya auku bai sake faruwa ba.
Sai da yaran makarantar islamiyyar suka shafe kwanaki 88 tsare a hannun ƴan bindiga suna shan azabar duka kafin maharan suka sako su.
Wasu daga cikin yaran da suka zanta da wakilin mu a garin Tegina sun bayyana cewa duk safe sai maharan sun jijjibge su sanna su basu fara shinkafa su ci.
Sannan kuma ledar ruwa daya ake ba mutum biyu su sha a duk rana. Haka suka rika rayuwa har Allah ya kai ga an sake su.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar Mohammed Idris ya yi karin haske game da matakan da gwamnati ta dauka domin n magance matsalar tsaro a jihar da kuma kare yaran makarantun jihar.
Sannan kuma ya ƙaryata raɗeraɗin da ake yaɗawa wai gwamnatin jihar ta bada kuɗi wajen biyan ƙudin fansa da ka baiwa ƴan bindiga.
” Ko sisi gwamnatin jihar Neja bata bada ba. Ba za mu ɗauki kuɗin da ya kamata ayi wa mutane aiki da su ba mu rika ba wasu da sunan kuɗin fansa bs Gwamnati ba ta ba ƴan bindiga ko sisi ba.
Discussion about this post