Mijina mayen mata ne, da ga ya ƙyallara ido ya hango mace ai kuma shikenan – Matan mai neman a raba aure

0

A kotun Igando dake jihar Legas ne wata matar aure mai suna Chima Udemi ta roki kotu ta amince da bukatar mijinta Tobechukwu na kotu ta raba auren su.

Chima da Tobi sun shekara 33 a gidan aure tare.

Chima ta bayyana cewa mijinta Tobechukwu mayen mata ne duk macen da ya ƙyallara ido ya gani shikenan ba zai samu natsuwa ba sai ya kwana da ita. Ni fa har da kanwata ya yi lalata.

Ta ce Tobechukwu na kwana da kanwata a cikin gidan da ta gina sannan ya hada da kawaye nabduk bai barsu ba.

Chima ta ce ta haifi yara bakwai da Tobechukwu sannan itace sutura, kudin makaranta, ci da sha a gidan.

“Na yi kokari na gina gidan kaina amma da yake Tobechukwu ya lallabo ya zo ya zauna tare da ni a gidana ina ciyar da shi Ina shayar da shi sannan duk da haka bai ishe shi ba sai ya rika kwana mun da kanwa da kawaye na.

Chima ta bayyana haka ne bayan Tobechukwu ya kai kara kotu a raba auren su.

A bayanin da ya yi Tobechukwu ya ce ita ma matarsa ba kanwar lasa bace domin ƙasurgumar mazinaciya ce domin ta gudu ta ƙyale shi da kula da ‘ya’yan su har na tsawon shekara 10.

“A shekarar 2020 Chima ta dawo dakinta bayan ta gama yawace yawacen ta da samarinta.

Alkalin kotun Adeniyi Koledoye bayan ya saurari ma’auratan biyu ya roke su su je su sasanta kan sa.

Koledoye ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 21 ga Satumba.

Share.

game da Author