Shugaban Ma’aikatan gwamnatin tarayya Folashade Yemi-Esan ta bayyana wa manema labarai a fadar shugaban Kasa cewa gwamnati ta amince daga yanzu maza su rika zuwa hutun makonni biyu a duk lokacin da matan su suka haihu.
Yemi-Esan ta kara da cewa gwamnati ta yi haka ne domin suma maza su sami damar dan sabawa dajaririn a lokacin da suke hutun.
” Ba tun yanzu wannan damar ke gaban mu, yanzu ya tabbata, maza suma za su rika samun hutun makonni 2 duk lokacin da matan su suka haihu. Hakan zai sa suma su dan saba da jaririn a lokacin da suke gida zaune.