MATSALAR TSARO: Na daina karɓar uzuri daga kwamandoji na, ku fita a yi ta ta ƙare kawai -Babban Hafsan Sojojin Najeriya

0

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya gargaɗi dukkan kwamandojin sojojin Najeriya cewa ya daina karɓar uzuri ko gazawa, saboda haka su tashi tsaye su kakkaɓe ɓatagari a ƙasar nan kawai.

Yahaya ya yi wannan kakkausan gargaɗin a wurin buɗe taron Manyan Hafsoshin Sojoji na watannin Afrilu zuwa Satumba, wanda ya gudana a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce sojojin Najeriya a ƙarƙashin sa za su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar samun hanyoyin kakkaɓe duk wani ƙalubale na matsalar tsaro a ƙasar nan.

Laftanar Janar Yahaya ya ƙara da cewa ya umarci kwamandojin sojojin Najeriya su ci gaba da ragargazar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, irin yadda ake ragargazar su a halin yanzu, ta yadda sun fara ɗaiɗaicewa.

Yahaya ya umarci a yi gagarimin farmaki a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, inda matsalar tsaro ta fi tsamari.

“Kwamandoji su kwana da tashin cewa su ci gaba da gagarimin aikin da su ke kan yi a yanzu.

“Ba zan karɓi wani uziri ko gazawa daga ɓangaren kwamandoji na ba. Gazawa duk yadda yake gazawa za’a kira ta, ba za a sake mata suna ko fenti ba.”

Ya ce ana nan ba da daɗewa ba za ƙara wa sojoji kayan aiki masu nagarta domin gudanar da aikin su.

Share.

game da Author