Manyan jami’an gwamnati ke sayen motocin da a ka yo sumogal ɗin su zuwa Najeriya – Hukumar Kwastan

0

Hukumar Hana Fasa-ƙwauri ta Ƙasa (Kwastan) ta bayyana cewa akasarin motocin Hilux da manyan jami’an gwamnati ke amfani da su, duk a hannun ‘yan sumogal su ke sayen su.

Mataimakin Babban Kwanturola Aluyu Saidu ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke bayani dalla-dalla a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya mai lura da Ayyukan Hukumar Kwastan, a ranar Talata, a Abuja.

Ya ce akasarin motocin Hilux na Ma’aikatu, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnantin Tarayya duk na sumogal ne.

Saidu ya wakilci Shugaban Hukumar Kwastan ta Kasa, Hameed Ali ne, inda aka gayyace shi domin yin bayani dangane da tsauraran matakan da ake bi kafin masu kaya su karɓi kayan su a hannun kwastan a manyan tashoshin ruwan ƙasar nan.

Ana ƙorafin cewa tsauraran matakan su na haddasa cinkoson kayayyaki a tashoshin jiragen ruwan Najeriya.

Da ya ke magana, Saidu ya ce akwai buƙatar kowa ya riƙa kiyayewa da dokokin da gwamnati ta shimfiɗa.

“Amma abin takaici, manyan jami’an gwamnati, ban ce ‘Yan Majalisar Tarayya ba – dukkan motocin da ake masu rakiyar tsaron lafiya, samfurin Hulux, na sumogal ne.

“Saboda idan mu ka duba kwamfutar da mu ke killace adadin samfuran motocin da ake shigowa da su ƙasar nan ta halastacciyar hanya, za mu ga cewa an rage shigo da Hulux sosai. Sai dai abin haushi ga su nan sabbi rangaɗau kowa na gani birjik a hannun manyan jami’an gwamnati, waɗanda aka shigo da su ta sumogal.”

Shugaban Kwamiti Keke Abejide ya yi masa tambihi dangane da cunkoso a tashoshin ruwa, inda ya nuna masa tsauraran matakan da kwastan ke ɗauka na haddasa cushewar kaya da haddasa cinkoson manyan motoci.

Saidu ya ce matakan da kwastan ke ɗauka 6 ne ba 18 ba, kamar yadda Majalisar Tarayya ta yi iƙirari.

A ƙarshe dai sun bayar da shawarar matakan da za a bi domin a samu sauƙi. Shi kuma Saidu ya ce za a yi amfani da matakan.

Share.

game da Author