Majalisar Tarayya ta nuna damuwa dangane da rashin sanin haƙiƙanin yadda aka yi da kadarorin da aka ƙwato daga tsoffin shugabannin ƙasar nan.
Kwamitin Lura da Kadarorin Gwamnantin Tarayya ne ya bayyana haka a lokacin da Babban Sakataren Kwamitin Ƙwato Kadarorin Gwamnanti a Hannun Ɓarayin Gwamnati (PIC), Bala Samid ya bayyana a gaban kwamitin a ranar Litinin.
Shugaban Kwamitin Majalisa Honorabul Ademorin Kuye, ya bayyana cewa sun gano cewa wasu kadarorin da aka ce an sayar, to ba a sayar da su ba.
Kuma kwamiti ya gano wasu gidajen da aka sayar ɗin har yanzu ba a biya kuɗaɗen ba.
Musamman kwamitin ya nemi a kawo masa bayanai dalla-dalla dangane da yadda aka yi da kadarori ko kuɗaɗen da aka karɓo waɗanda tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha ya kimshe a ƙasashen waje, sai daga baya lokacin wannan gwamnatin aka riƙa maido kuɗaɗen.
Kuye ya kuma ɗora alamomin tambaya akan yadda aka sayar da wasu kadarorin.
Ya ce sun gano har yanzu wasu akwai jama’a a ciki, ba su fita ba, alhali an shaida masu cewa gidajen babu kowa a cikin su.
Kwamiti ya kuma nemi sanin adadin kuɗaɗen da aka sayar da kadarorin, tare da gabatar masa da shaidar ko nawa aka saka a aljihun gwamnatin tarayya.
Babban Sakataren Kwamiti Bala Samid ya ce gidajen da har yanzu mazaunan su ba su tashi ba, sun kasa biyan haya ne, kuma a duk lokacin da aka yi ƙoƙarin fitar da su, sai su je kotu su samu umarnin hana fitar da su da tsiya daga kotuna daban-daban.
Ya ce ya na maraba da duk wani mataki da Majalisar Tarayya za ta ɗauka, domin a karɓo kuɗaɗen hayar da mazauna gidan su ka ki su biya.