Majalisar Kaduna ta tsige shugaban masu rinjaye na majalisar, Haruna Mabo, ya koma ɗan kallo

0

A zamar majalisar Kaduna ranar Laraba, mataimakin shugaban majalisar wanda ya jagoranci zamar majalisar a wannan rana ya bayyana cewa daga ranar an tsige Honorabul Haruna Mabo daga shugabantar masu rinjaye a majalisar.

Ya ce gaba daya yan majalisan dake karkashin jam’iyyar APC a majalisar sun amince a tsige Honorabul Haruna Mabo daga shugabancin mambobin majalisar masu rinjaye.

Haruna Mabo na daga ƴan gaban goshin gwamna El-Rufai da shigaban majalisar Jihar Kaduna, Yusuf Zailani.

Wannan sauyi da aka yi a majalisar ya nuna cewa lallai an samu mummunar ɓaraka a tsakanin jigajigan APC a majalisar Kaduna.

A baya bayan nan, majalisar ta sallami tsohon shugaban majalisar Aminu Shagali, bayan ya shafe kwanaki da doka ta bada bai zauna a majalisar ba.

Tuni har an yi zaben cike gurbin kujerar a Zariya sai dai kuma kash, APC bata yi nasara ba, PDP ce ta lashe kujerar.

Share.

game da Author