Majalisar Ƙolin Addinin Musulunci ta jinjina wa zaɓen Ƙananan Hukumomin Kaduna

0

Majalisar Ƙolin Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ta jinjina wa Gwamnatin Jihar Kaduna dangane da yadda ta shirya kuma ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi lami lafiya a jihar.

NSCIA wadda ke ƙarƙashin jagorancin Sultan Abubakar III, ta bayyana cewa yadda aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kaduna ya nuna nan ba da daɗewa ba, dimokraɗiyya za ta hau bisa turba mai inganci a faɗin ƙasar nan.

A ranar Asabar da ta gabata ce aka gudanar da zaɓukan ciyamomi da kansilolin jihar Kaduna.

An gudanar da zaɓen a ƙananan hukumomi 23. Amma kuma an ɗage zaɓukan a ƙananan hukumomi huɗu saboda dalilai na tsaro, har sai a ranar 25 Ga Satumba.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda jam’iyyar PDP ta buga Gwamna Nasir El-Rufai da ƙasa a akwatin Mazaɓar Unguwar Sarki da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa.

Hakan na nufin PDP ce ta lashe zaɓen kansilan Mazaɓar El-Rufai a Kaduna.

A zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomi 23, APC ta lashe 15, ita kuma PDP ta lashe ƙananan hukumomi biyu kacal.

Tun bayan dawowar mulkin dimokraɗiyya cikin 1999 dai jam’iyya mai mulki ce ke lashe dukkan zaɓukan ciyamomi da kansilolin jihohi.

Wannan ta sa jama’a ke ƙorafin cewa kamata ya yi a maida zaɓukan ciyamomi da na kansiloli a ƙarƙashin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), maimakon hukumar zaɓen da gwamnoni ke kafawa, wadda jama’a ba su ganin ta da wata daraja ko ta sisin kwabo.

Dangane da zaɓen ƙananan Kaduna kuwa, NSCIA ta bayyana cewa hakan na nuna akwai alamun haske a cikin dimokraɗiyya nan ba da daɗewa ba.

Majalisar ta tunatar da yadda a baya ake yin ɗauki-ɗora da tuwo-na-mai-na maimakon zaɓe a kowace jiha a lokutan zaɓen ƙananan hukumomi.

Daga nan NSCIA ta yi amfani da wannan dama wajen kira ga ɗaukacin Musulmai su riƙa gudanar da komai a bisa gaskiya, adalci, bayar da ‘yanci ga kowa da kuma bin umarnin Allah (SWT).

Share.

game da Author