Sakataren kungiyar Makiyaya ta kasa Haruna Tugga ya bayyana a wata sanarwa ranar Juma’a cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban kungiyar Miyetti Allah na Karamar hukumar Lere bubakar Danbardi bayan sun yi garkuwa da shi na tsawon makonni biyu.
Tugga ya ce maharan sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliya 20 amma kuma iyalan marigayin suka ce ba su da shi. Bayan harhadawa da suka yi suka samu naira 250,000 suka kuma kai wa maharan, bayan sun karba sai suka kashe shi kuma.
” Sun jefar da gwar sa a a mahadar Saminaka-Mariri-Zangon Kataf.
Akarshe tugga ya ce kungiyar Miyetti Allah ta kasa ta tura tawagar jaje ga iyalai da ‘yan uwa marigayin. Sannan kuma yayi kira ga jami’an tsaron jihar Kaduna su gaggauta kamo wadanda suka kashe Danbardi.