MACIJI ZAI SHIGA WANDO…..: Wane irin zaman tare za a sake yi tsakanin waɗanda ‘yan Boko Haram su ka lalata wa rayuwa da tubabbun ‘yan ta’adda?

0

Gwamnatin Tarayya ta daɗe da fito da shirin ta na kankare aƙidar ta’addanci a ƙwaƙwalen ‘yan Boko Haram, waɗanda sojoji ke kamawa da ran su da kuma masu miƙa wuya don kan su.

Shirin wanda ake kira ‘de-radicalization’ a Turance, da farko za a tattara su wuri ɗaya ne ana ba su lacca da nasihohi, tare da koya masu sana’o’in hannu, domin dogaro da kan su idan sun koma cikin al’umma, domin ci gaba da rayuwar su ta da can kafin shigar su harkar ta’addanci. Saboda tarairaya da tsarin ‘de-radicalization’ ya yi wa tubabbun ‘yan Boko Haram, har haɗa masu da ɗan jarin somin-taɓin fara sana’a tsarin ya tanadar.

Sai dai kuma cikin watanni uku zuwa yau ana ta samun tururuwar dandazon ‘yan Boko Haram da ke fitowa su na miƙa wuya, waɗanda aƙalla zuwa yanzu za su kai kusan 5,000.

Gwamnatin Tarayya ta tsaya kai da fata cewa yarjejeniyar ƙa’idar yaƙi ta duniya ba ta ce a zartas da hukunci a kan wanda ya miƙa wuya ya yi saranda ba.

Inda matsalar ta ke shi ne, idan ba a hukunta su ba, to ina makomar su kuma.

Saboda Gwamnantin Tarayya ta kasa tanadar masu da wata makoma, sai ta yanke shawarar sallamar su su koma ci gaba da rayuwa a cikin al’ummar da su ka lalata.

Wannan fa shi ake kira ‘maciji zai shiga wando’.

‘Yan Boko Haram ɗin waɗanda akasarin su ‘yan asalin Jihar Barno ne, sun tafka ɓarnar da munin ta ya kai ko bayyana ta ba son yi ake yi ba. Sun kashe dubban mutane, sun ƙona garuruwa da ƙauyuka. Sun dasa bama-bamai sun halaka dubban jama’a tare da naƙasa dubbai. Sun sace dubban yara ƙanana mata, sun ƙwace wa miji matar sa, sun ƙwace wa uba ‘ya’yan sa mata su na lalata da su.

Sun tarwatsa masallatai da coci-coci, sun kashe sojoji dubbai da ‘yan sanda. Sarakuna ba su tsira ba. Sun sace kayan abincin al’umma
Boko Haram sun tilasta wa miliyoyin ‘yan Najeriya zaman-dirshan a sansanonin gudun hijira.

Ba su da imanin tausaya wa duk wani da ba aƙidar su ɗaya ba. Allah kaɗai ya san yawan Musulmai da Kiristocin da Boko Haram su ka yi wa yankan-rago.

Babu wanda ya san yawan waɗanda su ka tsallake ƙasashe maƙwauta su na gudun hijira.

Dubban mata na nan Arewa su na ta gararambar bara da maula a kan titi ko cikin gidaje, sakamakon lalata masu rayuwa da Boko Haram su ka yi.

Ta fannin tattalin arzikin ƙasa kuwa, Boko Haram sun lalata Arewa, ba ma Barno da Yobe da Adamawa kaɗai ba. Allah kaɗai ya san kuɗaɗen da ake narkarwa a fannin tsaron ƙasar nan, saboda bala’in Boko Haram.

Duk bayan sun yi wannan ɓarna, kuma ba su gama ba, domin ana kan yaƙin har yanzu, sai kuma bayan matsalar yunwa ta kassara su, sun fito sun miƙa wuya, sai a kira su tubabbu?

Boko Haram: Macijin Da Bai Mutu Ba, Ballantana A Datse Kan Sa:

Al’ummar Jihar Barno da ke kaffa-kaffa wajen karɓar tubabbun ‘yan Boko Haram, su na da hujjar su. Tun farko dai aƙida ce mummuna su ka fara amfani da ita a matsayin hujjar halasta jinin duk wanda bai yarda da ta su aƙidar ba.

Ya kamata duk mai hankali ya tambayi gwamnati, shin ina makomar aƙidar da Boko Haram su ka kafu a kan ta? Sun yi watsi da ita, ko kuwa har yanzu ta na cikin zukatan su? Ina makomar litattafan da su ke kafa hujja da su har su ke halasta jinin musulmi da kuma halasta wa junan su matan musulmai waɗanda ba aƙidar su ɗaya ba?

Miliyoyin al’umma sun faɗa cikin rayuwar ƙuncin da har abada babu mai iya kankare masu bala’in da Boko Haram su ka jefa su.

Su na cikin wanann mummunar rayuwa kuma sai a wayi gari a sako masu dubban matasan da su ka jefa su cikin wannan bala’i, a ce a manta da komai?

Anya gwamnati ba ta gudun kada masu ɗaukar fansa a cikin al’umma su bayyana?

Shin su masu tubar, akwai tabbacin tubar watsar da aƙida ce, ko kuwa tubar-muzuru ce.

Ya rayuwar tubabbun za ta kasance idan su ka wayi gari a cikin al’umma su na neman abinci da kyar, saɓanin lokacin da su ke daji su na kama dabbobin jama’a da kayan abincin su, su na ci su ƙoshi?

Tambayar ƙarshe ga gwamnati, su waɗannan tubabbun ga gwamnati kaɗai su ka tuba, ko kuwa har ga Allah tubar ta su ta jiɓinta?

Kada fa a sakar wa al’umma maciji a cikin wando bayan an ɗaure masu hannayen kisan macijin!

Share.

game da Author