Zargi: Wani labari a shafin Facebook ranar 24 ga watan Agusta ya ce N-Power ta fara tantance sunayen wadanda za su sami kudaden bana.
Wani mai suna Badarubala TV a shafin facebook mai ma’abota 100 ya wallafa labarin da ya sanar da jama’a cewa hukumar N-power ta fara tantance sunayen wadanda za su sami kudaden tallafawa matasa na tsawon shekaru biyu masu zuwa. Labarin wanda ya fito ranar 24 ga watan Agusta an yi masa taken “Breaking News” ko kuma labari da dumi-dumin sa.
Labarin ya bukaci mutane su yi amfani da wasu lambobin da aka rubuta domin ganin ko sun yi nasara ko ba su yi ba. Tun da aka wallafa labarin, mutane 50 sun sake sassakawa a sahfukan su da na abokansu.
Tsokacin da sharhin ya yi na cewa “Na duba amma na sami sakon cewa, ba’a gano bayanan da na bayar ba.” Wannan tsokaci da taken “Breaking News” (abin da ya sa labarin ya yi kama da irin wadanda suka cika kasancewa “fake news” labaran karya)ya sa muke so mu yi cikakken bincike.
Tantancewa
Da muka fara binciken, Dubawa ta gano rahotanni a thenationonlineng da legit.ng sun tabbatar da labarin
Kafofin yada labarai biyu sun ruwaito cewa ranar 23 ga watan Agusta, ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta sanar cewa za’a kaddamar da kashi na uku a birnin Tarayya wato Abuja.
Farouq ta ce an zabi mutane 450,000 a cikin mutane miliyan 6 da suka nuna sha’awa za su sami tallafin ne a karkashin sashen wadanda suka kammala jami’a. Ta kara da cewa kudin, wato dalan Amurka 45, 665 zai taimaka musu da abin da suke bukata wajen samunbayanai.
Shafin N-Power ya sake tabbatar da sahihancin labarin inda shafin ya bayyana cewa duk wadanda su ka ga sunayensu, su yi kokari su je su tabbatar da bayanan su domin su kammala matakin karshe na samun kudin.
Bacin haka, Joshua Ezra wanda na daya daga cikin wadanda su ka nemi tallafin na N-power ya tabbatar da hakan kuma ya ce tun watan Yuni aka fara tantance sunayen.
“ Ranar litini aka fara. Tun watan Yuni suke tantance sunayen wadanda suka nemi tallafin. Wannan karon, an riga an fara shirin amma kuma ba’a riga an tura mu wurin da ya kamata mu je mu yi aiki ba,” ya ce.
A Karshe
Zargin Badarubala TV cewa N-Power ta kammala tantance sunayen wadanda za ta baiwa tallafin gaskiya ne.
Discussion about this post