Shugaba Muhammadu Buhari ya sake aika wa Majalisar Dattawa wasiƙa a karo na biyu domin don yin canji a sabuwar Hukumar Kula da Ayyukan Haƙo Ɗanyen Man Fetur (NPRA).
Ya aika da wasiƙar neman amincewar Majalisar Dattawa ya cire sunan Sarki Auwalu, inda ya maye gurbin sa da Farouk Ahmed.
An canja sunan Sarki Auwalu ne bayan an aika da sunan sa a ranar 16 Ga Satumba domin amincewa.
Sai dai kuma Buhari ya canja sunan sa da na Farouk Ahmed, kwanaki uku bayan PREMIUM TIMES ta fallasa yadda wasu makusantan Buhari su ka nunke shi baibai, a ƙoƙarin su na ganin sun yi kaka-gida a harkokin haƙo ɗanyen man fetur a Najeriya.
Buhari bai bayyana wa Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan dalilin maye sunan Auwalu da na Ahmed ba.
Ya dai rubuta cewa ya yi hakan bisa ƙa’ida, kamar yadda Dokar Fetur Sashe na 34 (3) ta 2021 ta tanadar.
Ga Labarin Da Premium Times Ta Buga Dangane Da Hukumar:
Yadda makusantan Buhari su Sabi’u Tunde ke shirya tuggun maida hada-hadar fetur ɗin Najeriya ‘kayan-gado’.
Fannin harkokin haƙo ɗanyen man fetur a Najeriya na neman faɗawa hannun wasu ‘yan gidogar da ke da kusanci da Shugaba Muhammadu Buhari, yayin da su ka tsoma dungulmin hannayen su wajen ganin an yi carafken daƙa-daƙa wajen naɗin Shugabannin Hukumomin Kula Da Ayyukan Haƙo Fetur wato ‘Upstream’, ‘Midstream’ da kuma ‘Downstream’.
Sabbin hukumoni ne guda biyu aka ƙirƙiro a ƙarƙashin Sabuwar Dokar Fetur (PIA), wadda Shugaba Buhari ya sa wa hannu kwanan farkon watan Agusta.
A Majalisar Tarayya da cikin ƙasa ana nuna damuwa ganin yadda waɗannan makusantan Buhari ke amfani da kusanci da shi, ba tare da sanin sa ba, su ke ƙoƙarin yi wa ɓangaren ‘Upstream’ kaka-gida, ganin cewa shi ne mafi muhimmanci a kan ‘Midstream’ da ‘Downstream’.
Ma’anar Hukumomin ‘Upstream’, ‘Midstream’ Da ‘Downstream’:
A ranar 16 Ga Satumba Shugaba Muhammadu Buhari ya sake aika wasiƙa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, inda ya nemi a amince masa ya naɗa Shugabanni da Mambobin Hukumar Gudanarwa ga hukumoni biyu da su ka haɗa da:
1. Upstream Regulatory Commission.
2. Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority.
Upstream Regulatory Commission na nufin Hukumar Kula da Ayyukan Haƙo Ɗanyen Man Fetur da Gas Daga Ƙarƙashin Ƙasa.
Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority kuma na nufin Hukumar Kula da Sufurin Kayan Mai da Sarrafa Ɗanyen Mai Zuwa Fetur, Gas, Man Shafa, Giris, da sauran nau’o’in man da ake sarrafawa daga ɗanyen mai.
Yadda Aka Shigar Da Son Zuciya Wajen Naɗa Muƙamai:
Wasu ‘Yan Majalisar Tarayya su biyu sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa akwai damuwa sosai wajen yadda aka ƙudunduno sunayen shugabannin hukumomin aka gabatar, domin majalisa ta amince da su. Musamman idan aka yi la’akari da fannin da kowanen su ya fi ƙwarewa a kai, kafin a miƙa sunan na sa.
Birbiri Da Kan Jemage:
Sarki Auwalu, wanda a yanzu shi ne Daraktan Sashen Kula da Albarkatun Mai, inda ya ke da ƙwarewa da gogewar fiye da shekaru 20 a ɓangaren ayyukan haƙo ɗanyen mai (Upstream), sai aka bada sunan sa a matsayin wanda za a naɗa Shugaban Hukumar ‘Midstream’ da ‘Downstream’ Commission.
Shi kuma Gbenga Komolafe, wanda a yanzu shi ne Babban Manajan Harkokin Sayar da Ɗanyen Mai, aka bada sunan sa a matsayin sabon Shugaban Hukumar ‘Upstream’ Commission.
Masana kuma jami’an NNPC sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa Komolafe ya fi dacewa da Hukumar Midstream and Downstream Regulatory Authority, ba Upstream Regulatory Commission ba.
Discussion about this post