Gwamnatin jihar Legas ta yi kira ga masu hada magungunan gargajiya da su kawo wadanda suka hada na Korona a duba a tantance su ko a dace
a samu wanda zai warkar da cutar.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi wannan kira ne a taron ranar maganin gargajiya ta shekaran 2021 da aka yi ranar Talata a dakin taro na Adeyemi Bero, Alausa, Ikeja, Legas.
Taken taron na 2021 shine: “Magungunan Gargajiya: Bincike domin samun ci gaba”.
Sanwo-Olu wanda Kwamishinan Lafiya, Akin Abayomi ya wakilce shi a taron ya yi kira ga masu hada magungunan gargajiya da su hada hannu da masu hada maganin bature domin ganin nasu maganin da suke hadawa ya samu karbuwa da inganci.
Ya ce gwamnati a shirye take ta mara masu baya wajen samun nasara a wajen harhada magungunan gargajiya.
“ Har yanzu Afirka ba ta hada maganin warkar da cutar korona ba. A dalilin haka nake kira ga masu hada maganin gargajiya da su kawo magungunan da suka hada a tattance su.
Jihar Legas na daga cikin jihohin da korona ta yi tsanani a cikin sa.
Mutum 72,918 ne suka kamu kuma cutar ta yi ajalin mutum 604 a jihar.
Sanwo-Olu ya kuma hori masu hada maganin gargajiya a kasar nan da su hada magunguna da za su inganta kiwon lafiyar mutane ba maganin da zai cutar da lafiyar su ba.
A jawabin sa da yayi a wajen taron, Shugaban Hukumar Kula da Magungunan Gargajiya na Jihar Legas (LSTMB), Adebukunola Adefule-Ositelu, ta ce lokaci ya yi da za a inganta magungunan gargajiya ta yadda suma za a rika bugun kirji da su wajen warkar da marasa lafiya kamar na asibiti.
Adefule-Ositelu ta yi kira ga masu hada maganin gargajiya da su inganta aiyukkan su ta yadda mutane a kasar nan za su amince da su idan bukatar neman magani ya taso
Discussion about this post