Ku daina furta kalaman da ka iya hargitsa Najeriya – Gargaɗin Gwamnati ga shugabanni

0

Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi shugabannin siyasa da na addini su daina furta kalaman da ka iya hargitsa kasar nan kamar wutar daji.

Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ne ya yi wannan gargaɗin, lokacin da ya ke magana da Kamfanin Dillancin Labarai a Tsibirin Sal na Cape Verde.

Minista Lai ya je Cape Verde domin halartar Taron Hukumar Buɗe Ido ta Majalisar Ɗinkin Duniya na 64.

Lai ya ja kunnen kafafen yaɗa labarai musamman talbijin da radiyo waɗanda ya ce su ne ke ruruta wutar kalaman tayar da hankali, cewa su riƙa gudanar da aikin su bisa tsarin da aikin su ya gindaya.

“Makonni biyu da su ka gaba kafafen yaɗa labaran Najeriya musamman talbijin sun shagala da yaɗa kalaman da ke iya hargitsa ƙasar, tamkar wutar daji.

“Irin waɗannan kalaman tayar da zaune kan fito daga shugabannin siyasa da na addini da kuma wasu masu sharhin al’amurran yau da kullum a cikin jama’a. Munin kalaman su zai iya haddasa gobarar daji a cikin ƙasar mu Najeriya.

“Saboda kalaman su na haɗa husuma tsakanin wannan ƙabila da waccan, ko mabiya wancan addini da wannan.”

Daga nan sai Minista Lai ya buga misalin irin wannan kalamai da abin da ya faru a Ruwanda, inda wani gidan radiyo da wata mujalla su ka haddasa kashe-kashen da aka yi asarar rayuka fiye da 800,000 a cikin 1994.

Share.

game da Author