Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wani matashi mai shekara 28 sannan ta maka shi a kotu bisa laifin kwarara wa wani dan sanda zagi a lokacin da ya ke aiki.
‘Yan sanda sun maka matashin mai suna Lekan Sebanjo a kotun Karu Grade1 ranar Juma’a.
Bayan sauraren karar da ‘yan sandan suka shigar alkalin kotun ya kama Sebanjo da laifin hana jami’an tsaron gudanar da ayyukan su.
Sai dai kuma Sebanjo ya musanta aikata haka.
Lauyan da ya shigar da karar Ayotunde Adeyanju ya ce hakan ya faru ranar 15 ga Agusta.
Adeyanju ya ce a wannan rana ‘yan sanda sun kama Sebanjo bayan sun tsayar da motarsa domin binciken takardun sa da abubuwan dake ke cin motar.
“Fitowar sa ke da wuya sa Sebanjo ya rika surfa wa dan sandan zagi. Ta inda ya ke shiga ba ta nan yake fita ba.
Alkalin kotun Anas Isa ya bada belin Sebanjo akan naira 500,000 tare da gabatar da wadanda za su tsaya masa biyu.
Za a ci gaba da shari’a ranar 6 ga Oktoba.