A ranar Laraba ne babban kotu a Lokoja jihar Kogi ta yanke wa Danladi Ichado hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta kama shi da laifin kashe wasu mata biyu da adda.
Alkalin kotun Justice Nicodemus ya ce ya yanke wannan hukunci ne bayan shaidan da Rekiya Rilwan wacce abin ya faru a idonta ta bada a kotun.
Lauyan da ya shigar da karar Inedu Opaluwa ya ce Ichado da yake zama a karamar hukumar Odogomu, Ankpa ya kashe wadannan mata ranar 6 ga Yunin 2020.
Opaluwa ya ce a wannan rana Ichado ya afka wa wasu mata uku Rabiatu Yusufu, Jamila Yakubu da Rakiya Rilwan a hanyar zuwa gona a kauyen Oko-Ojuwo, Ogaji.
Ya ce Ichado ya sari Rabiyetu Yusufu da Jemila Yakubu a kai da kirji da adda.
“Ga dukan alamu Ichado ya kai wa wadannan mata hari domin ya kashe su ganin cewa ya far wa matan da adda da ya ji musu mummunar rauni a jikinsu.
“Bayan ya kashe matan Ichado ya gudu amma jami’an tsaro sun kamo shi daga baya.
Opaluwa ya gabatar da shaidu uku da addar da Ichado ya yi amfani da shi wajen kashe matan.
Sai dai Ichado ya karyata haka yana mai cewa a lokacin da hakan ya faru yana gida yana aikin gyarar kwakwa.