Mai Shari’a Fadaunsi Adefioye ya bada umarnin a tsare Abodunri Ohai, bayan an same shi da laifin taimaka wa mai laifi guduwa.
Tun da farko dai an bayar da belin wanda ake zargi da sata da fashi, mai suna Olatunbosun ga Abodorin Ohai a kan kuɗi naira 100,000. Amma sai ya arce.
Da mai belin da aka tsare da wanda ya tare ɗin dai duk ‘yan’uwan juna ne, wa da ƙane.
Mai karɓar beli Ohai ya amsa wa kotu laifin sa na taimaka wa wanda ake zargi da laifin sata tsarewa.
A kan haka bayan kotu ta bada umarnin tsare shi, ta ce za a ci gaba da shari’ar a ranar 13 Ga Oktoba.
Kotun dai ta tsare bayan da ya kasa gabatar da wanda ya karɓi belin sa kan kudin beli Naira 100,000.
Abodurin mai shekaru 47 bai yi ja-in-ja ba, a lokacin da mai gabatar da kasa Clement Okunmose ya karanto masa caje-caje da tuhumar da ake yi masa.
Mai gabatar da ƙara ya ce laifin sa ya saɓa da Dokar Ƙasa Sashe na 107 da na 97. Kuma ya kawo cikas wajen hana shari’a ta yi aikin ta.