Kotun majistare dake Ado Ekiti jihar Ekiti ta yanke wa Emmanuel Bejide, mai shekaru 40, hukuncin zaman gidan yari saboda ana zargin sa da yin lalata da ‘yarsa.
Alkalin kotun, Mojisola Salau ta ce Bejide zai yi zaman gidan yari har sai kotun ta kammala yin shawara da fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na jihar.
Dan sandan da ya shigar da kara a kotu Sodiq Adeniyi ya ce Bejide ya fara lalata da ‘yarsa mai shekara 17 dake ajin karshe na babban sakandare tun a shekarar 2020 a Ikere Ekiti.
Adeniyi ya ce yarinyar ta bayyana wa jami’an tsaro cewa a watan Satumba Bejide ya kai ta wani Otel dake Akure jihar Ondo inda a nan ya yi mata alkawarin kai ta kasar Malaysia idan ta amince da shi.
Ya ce rundunar ta kama Bejide bayan ‘yar ta kawo kara ofishinsu ranar 21 ga watan Agusta.
Alkali Mojisola ta ce za a ci gaba da shari’a ranar 16 ga Satumba.
Idan ba a manta ba a watan Yuni PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta damke wani mutum mai suna Durodola Ogundele dake da shekaru 65 akan zargi yi wa matar mahaifinsa mai shekaru 85 fyade.
Kakakin rundunar Sunday Abutu ya ce bisa ga labarin da rundunar ta samu Ogundele ya shiga dakin dattijiyar kuma matar mahaifinsa dake fama da ciwon kafa domin ya shafa mata magani a kafan ta inda daga shafa magani kuma sai ya aikata abinda ya so da karfin tsiya.