A ranar Alhamis ne kotu a Iyaganku, Ibadan ta yanke hukuncin daure wani birkila mai suna Azeez Salau mai shekara 26 a kurkuku bayan an kama shi da laifin yin lalata da kurma mai shekara 20.
Alkalin kotun Mercy Amole–Ajimoti ta yi watsi da rokon sassauci da Salau ya nema sannan ta ce za a daure shi har sai kotu ta kammala yin shawara da fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na Oyo jihar.
Za a ci gaba da shari’a ranar 30 ga Nuwanba.
Lauyan da ya shigar da karar Philip Amusan ya bayyana cewa Salau mazaunin Ile Tuntun area a Academy dake garin Ibadan kuma yana da mata da da daya.
Amusan ya ce a watan Yuli Salau ya yi wa kurmar Kemi Omotola mai shekara 20 dake aikin shara da wanke-wanke a Atagba fyade.
Yakan jira ta ne sai ta gama aiki a gidan da ta ke yi sai ya lallaba ya danneta da karfin tsiya yayi lalata da ita.