Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi BSPHCDA, ta bayyana cewa ta karbi kwalaben maganin rigakafin Korona na AstraZeneca guda 21,000.
Shugaban hukumar Rilwanu Mohammed ya sanar da haka ranar Lahadi da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.
Mohammed ya ce BSPHCDA ta karbi kwalaben maganin daga hukumar NPHCDA da ya gabata wanda kungiya mai zaman kanta The Society for Family health’ ta kawo wa hukumar a makon da ya gabata.
Ya ce NPHCDA ta bai wa BSPHCDA kwalaben maganin rigakafin ne domin yi wa mutanen rigakafin korona zango na biyu.
” Sau biyu allurar rigakafin Korona na AstraZeneca guda biyu ake yi wa mutum domin samun kariya daga kamuwa da cutar.
Idan ba a manta ba a ranar Litinin din da ya gabata ne gwamnati ta fara yi wa mutane allurar rigakafin korona zango na biyu da maganin rigakafin na ‘Moderna’ wanda kasar Amurka ta bai wa kasar nan kyauta.
Bayan haka gwamnati ta kuma karbi kwalaben maganin rigakafin na Johnson & Johnson guda 177,600 daga hannun AU.
Daga nan gwamnati ta karbi kwalaben maganin rigakafin na Oxford-astraZeneca guda 699,760.
Gwamnati ta ce za ta yi amfani da maganin Oxford-astraZeneca da ta karba domin karike yi wa mutanen da suka yi allurar rigakafin da ruwan maganin a zango na farko.
Zuwa yanzu an yi wa mutum 3,966,005 allurar rigakafin cutar korona a kasar nan inda daga ciki mutum sama da miliyan biyu sun yi. allurar rigakafin zango na biyu.
Gwamnati ta yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da korona domin samun kariya.
Sannan gwamnati ta yi kira ga wadanda basu yi allurar rigakafin korona ba da su hanzarta zuwa wuraren da ake yin rigakafin domin kare kansu da na kusa da su daga kamuwa da cutar.
Discussion about this post