Ko kukan jini Gwamnoni 36 za su yi, sai an biya mu la’adar Naira biliyan 172 daga asusun su -Ted Nwoko

0

Wani uban gada-gada kuma tsohon ɗan majalisar tarayya, sannan kuma hamshaƙin biloniya, Ted Nwoko, ya rubuta wa Ministan Shari’a Abubakar Malami wasiƙa, mai ɗauke da yin tofin tir ga wasiƙar da Gwamnonin Najeriya 36 su ka aika wa Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed, inda su ka nemi kada ta biya ‘yan gada-gadar gidoga dala miliyan 418, waɗanda Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun amincewa a biya su, ba tare da neman shawarar gwamnonin ba.

Nwoko wanda shi ma lauya ne, ya aika da wasiƙar ta hannun lauyan sa Joe Gadzama, inda ya bayyana wa Antoni Janar Malami cewa wasiƙar gwamnonin cike ta ke da jahilcin yadda aka yi har ‘yan gidogar su ka cancanci a biya su kuɗaɗen a matsayin la’adar ayyukan da su ka yi wa jihohin Najeriya da ƙananan hukumomi 774 a baya.

Ted Nwoko wanda ya ce kuɗaɗen idan an biya, shi ke da dala miliyan 142 a cikin dala 418 da za a biya, ya ƙara da cewa ko kukan jini gwamnonin Najeriya za su yi, sai an ɓamɓarar masa kuɗin sa daga asusun su an biya shi.

Ted dai ya aika wa Malami wasiƙar a ranar 6 Ga Satumba, 2021, tare da nuni da cewa babu wani umarni ko hukunci a kotu wanda ya dakatar a biyan sa haƙƙin sa.

Cikin watan Agusta ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya yi biris da shawarar gwamnonin Najeriya, ya rattaba hannun amincewa a biya ‘yan gada-gadar su shida dala miliyan 418, kwatankwacin fiye da Naira biliyan 170.

Hannun da Buhari ya rattaba ne ya sa Ministar Harkokin Kuɗaɗe ta umarci Ofishin Kula da Basussuka na Ƙasa (DMO) cewa ya bai wa ‘yan gada-gadar takardun alƙawarin biyan su basussukan cikin shekaru 10.

Bibiyar Musabbabin Kwatagwangwamar Gwamnoni 36 Da ‘Yan Gada-gada 6:

Gwamnoni 36 sun gargaɗi Ministar Kuɗaɗe kada ta biya ‘yan gidoga’ kuɗaɗen.

Gwamnonin Najeriya 36 sun rubuta wa Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed Wasiƙa, inda su ka gargaɗe ta cewa kada fa ta sake ta biya dala miliyan 418 ga ‘yan kwangilar da gwamnonin su ka ce ‘yan gidoga na gidi.

Wasiƙar dai sun rubuta ta ne ta hannun lauyan su Femi Falana, wanda ya rubuta mata hatsarin da ke tattare da biyan kuɗaɗen.

Falana ya nemi a madadin gwamnonin cewa Minista Zainab ta janye umarnin da ta ba Ofishin Kula da Basussuka (DMO) cewa ya fara shirin bayar da takardun alƙawarin biyan kuɗaɗen a cikin wasu ƙayyadaddun lokuta ga ‘yan kwangilar.

Gwamnonin sun ce ya kamata Minista Zainab ta fahimci cewa sun shigar da ƙara a Kotun Ƙoli, kuma Kotun Ƙoli ba ta ce a biya kuɗaɗen ba, domin harƙalla ce da dungu da gidoga kawai.

Kuɗaɗen waɗanda dala miliyan 418 ne, idan aka canja su zuwa dala a farashin gwamnati na dala 1 Naira 410, za su kama naira biliyan 171 kenan.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga yadda Buhari ya yi fatali da shawarar Gwamnoni 36, ya amince a biya dala miliyan 418 da su ka ce gidoga ce ba bashi ba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun amincewa a biya wani bashin da aka yi iƙirarin ana bin jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774.

Adadin bashin ya kai dala miliyan 418, kwatankwacin naira biliyan 159 da ya amince a biya wasu mutum shida, duk kuwa da cewa Gwamnonin Najeriya sun daɗe su na nuna wa Buhari cewa babu tabbaci ko wata ƙwaƙƙwarar shaida ko hujjar an yi ayyukan a jihohi har na waɗannan adadin maƙudan kuɗaɗe.

A ranar Talata PREMIUM TIMES ta ci karo da wani umarni da Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ta bai wa Ofishin Kula da Basussuka (DMO), cewa ya fara bayar da takardar alƙawarin biyan kuɗaɗe ga waɗanda su ka yi iƙirarin cewa su na bin jihohin da ƙananan hukumomi waɗannan kuɗaɗen.

Hakan dai ya na nufin Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba amincewa a biya bashin kenan.

Wannan mataki da Buhari ya ɗauka ya saɓa da shawarar da Gwamnonin Najeriya su ka sha bayarwa cewa a fara gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike a ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan, domin a tabbatar da sahihancin ayyukan da masu iƙirarin bin bashin su ka ce sun yi, amma ba a biya su ba.

Share.

game da Author