KIRA GA GWAMNA BADARU: Ka tuna da Ɗaliban Jigawa, suna cikin matsi, Daga Adamu Maiɗalibai

0

Na san dayawa daga cikin daliban jigawa da suka dogara da tallafin karatu domin biyan kudin makaranta, na san daliban jigawa dayawa wanda suke amfani da kudin domin cin abinci, na san daliban jigawa dayawa da suka dogara da kudin domin siyan kayan karatu saboda su tsira da mutuncin su.

Mai girma gwabna, a irin wannan lokacin da rayuwa tayi tsada, tattalin arziki ya karye, kudin makaranta ke cigaba da karuwa, hanyoyin samu ya ragu babu wani abu da dalibai suke da bukata daga gareka da ya wuce biyansu wannan kudade da basu taka kara sun karya ba.

Dayawan iyaye sun hakura da daukar nauyin yayansu kan harkokin ilimi saboda halin matsi da aka tsinci kai, wannan yasa wasu daliban suke kokartawa wurin daukar nauyin kansu kan harkokin karatunsu, Sai gashi har kawo yanxu ba’a biya wannan yan kudaden ba.

Na tuna shekaru biyu da suka gaba ta da kuma yadda nayi namijin kokari wurin samowa dalibai wannan yan kudaden Wanda a karshe ka saurareni ka biya wannan kudin, wannan ya tabbatar min da cewa nayi kokari Kuma na sauke nauyin dake kaina na shugabanci, kuma zan iya tsayawa dalibai bama iya gabansu ba a’a harma gaban gwamnati, sai dai kash tun lokacin baka sake waiwayen daliban ba.

Ina tambayar kaina wasu yan tambayoyi kamar haka

1) Shin gwamnati ta manta da dalibai ne?
2) Shin babu jagororin dalibai ne?
3) Shin su daliban basu da wata murya ne, meyasa basu daga ta har tazo kunnenka?
A karshe dai naji kunya gaba daya domin babu amsa.

Mai girma gwabna, mun sani yana cikin alkawarin ka cewar zaka kula da dalibai da ilimi, kana so mu yadda gaskiya ne kuma baka bamu kunya ba?

Ka tuna akwai wani yini domin hisabi, a wannan yinin mai zaka cewa Allah idan ya tambayeka kan dalibai?

Adamu Saleh maidalibai kazaure
salehadamu90@gmail.com

Share.

game da Author