A yanzu dai a ƙasar nan yaro na goye ne kaɗai bai san cewa hada-hadar ‘crypto’ babbar harka ce a Najeriya ba.
Ta kai ma Najeriya na a sahun gaban ƙasashen da aka fi yin hada-hadar ‘bitcoin’ a duniya. A kullum ‘yan ‘crypto’ sai ƙara afkawa su ke cikin wannan hada-hadar samun kuɗi ba tare an sharce gumin riga ko gumin goshi ba.
Bankin CBN Ya Hana ‘Crypto’ A Najeriya, Amma An Ƙi Bari:
Babu wata doka takamaimen da ke cikin kundin tsarin mulkin Najeriya wadda ta hana kasuwancin ‘bitcoin’, sai dai kuma a farkon wannan shekara ta 2021 Bankin Najeriya (CBN), ya fitar da sanarwar hana kasuwancin crypto. Sai dai kuma maimakon jama’a su daina, sai ma ƙara tsunduma cikin harkar su ke ta yi afujajan.
A ranar 5 Ga Fabrairu ce CBN ya fitar da kakkausar sanarwa ga Bankunan Kasuwanci na Najeriya cewa su daina mu’amala da duk wani mai sayen ƙwandalar crypto a bankunan su.
Sanarwar ta kuma gargaɗi bankunan cewa su kulle asusun ajiyar duk wani mai hada-hadar ‘bitcoin’ a bankunan su.
CBN ta gargaɗi bankunan cewa duk wani bankin da ya karya umarnin sa, za a ci shi tarar da sai ya riƙa kuka saboda tsananin yawan tarar.
Yayin da CBN ya nuna cewa bai hana mai kasadar hada-hadar ‘bitcoin’ ya yi abin da ba, amma dai ya hana bankunan kasuwanci zama tsani ko dillancin harkar, saboda cewar CBN a ƙarƙashin hada-hadar ‘crypto’ ko ‘bitcoin’ a taƙaice, ana harƙalla da haramtacciyar hada-hada da kuma damfara sosai. Musamman domin kasuwanci ne ake yi a duhu, babu sunayen masu hada-hadar a bayyane.
Sai dai kuma wannan zare idanu da gwamnatin tarayya ta yi bai hana jama’a ƙara tinjima cikin hada-hadar ba.
‘Yan ‘Crypto’: Kome Ta Fanjama, Fanjam!
Duk da gargaɗin Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin CBN, ‘yan Najeriya sun ɓullo da wata hanyar hada-hadar P2P irin su Remitano.
A ƙarƙashin wannan tsari na P2P, ba za ta sayi BTC da Naira ba, sai dai ka saya daga hannun wani daban.
P2P ya zama kamar wani dandalin haɗa masu saye da masu sayarwa a wuri ɗaya.
Saboda hada-hadar ‘bitcoin’ ta tsarin P2P ta na da wahalar toshewa ga cibiyoyin kula da hada-hadar kuɗaɗe na gwamnati.
Jama’a da dama na yi kasuwancin ‘crypto’ saboda lalacewar darajar Naira a kasuwar hada-hadar canjin kuɗaɗe.
Yanzu haka ta kai a duniya har Remitano ya ƙirƙirar ƙwandalar sa mai suna RENEC, domin inganta hada-hadar tsarin sa ga kwastomomin sa.
Kwanan baya wannan jarida ta buga labarin yadda Gwamnatin Amurka ta horas da masu bincike 50 na Najeriya dabarun toshe damfara a hada-hadar ‘cryptocurrency’.
Mahukuntan Amurka sun horas da masu bincike har mutum 50 ‘yan Najeriya. An koya masu dabarun daƙile damfara a hada-hadar zamani ta ‘cryptocurrency’.
Wannan bayanin na ƙunshe ne a cikin wani bayani da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta bayyana a cikin shafin ta na Twitter, a ranar Alhamis.
Horaswar da aka yi masu a tsarin daga-nesa, wato ‘virtual’, ta ta’allaƙa ne kacokan a kan yadda ake gane harƙalla a tsarin hada-hadar ‘bitcoin’, wato ‘cryptocurrency’.
An gudanar da horaswar da haɗin-guiwar Hukumar Binciken Amirka (FBI), Ofishin Jakadancin Amirka da ke Kenya, Addis Ababa, Ofishin Jakadancin Amirka da ke Najeriya da kuma Shirin Gwamnantin Amirka kan yaƙi da hada-hada da cinikin muggan ƙwayoyi a duniya.
Haka kuma waɗanda aka bai wa horon su 50 ‘yan Najeriya, jami’ai ne da su ka haɗa da masu shigar da ƙara ko masu gabatar da ƙarar masu aikata laifuka, waɗanda za su iya gabatar da masu damfarar ‘cryptocurrency’ a kotu.
Hada-hadar ‘bitcoin’ dai tsari ne da ake sayen ƙwandalar zamani, ta yadda za a iya saye da sayarwa da kuɗaɗen. Kuma ana yin hada-hadar don riba.
Premium Times ta buga labarin yadda darajar ‘Bitcoin’ ta haura dala 50,000 bayan karyewar da ƙwandalar ta yi cikin watan Afrilu.
Darajar ƙwandalar hada-hadar ƙuɗaɗe ta ‘Bitcoin’ ta sake tashi zuwa sama da dala 50,000 a duniya, a ranar Litinin, bayan karyewar martabar kuɗin, watanni uku da su ka gabata.
Ƙwandalar a ranar Litinin wajen ƙarfe 2:20 na yamma ta kai dala 50,274.68 daidai agogon Najeriya.
Hakan ya faru ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Amirkawa za su ƙara narka kuɗaɗe hada-hada, ta yadda za a ƙara samun riba.
‘Bitcoin’ ya ƙara daraja da kashi 2.84 cikin sa’o’i 24. Wato kashi 6.25 kenan a kowane mako.
Yayin da ƙarfin jarin ‘Bitcoin’ a kasuwannin hada-hada a yanzu ya kai dala biliyan 31,449,905,210.17. Wato ya ƙaru kenan da kashi 8.49 bisa adadin sa na baya.
Cikin watan Afrilu ne dai darajar hada-hadar amfani da ‘Bitcoin’ ta yi ƙasa warwas, inda a ranar 14 Ga Afrilu ya yi ƙasa, bayan ya kai dala 64,863.10.
Shi ma farashin cyrptocurrency na Ether ya tashi da kashi 2.8, wato ya kai dala 3,337.
Hakan na nufin ya tashi da kashi 91 bisa 100, bayan ya yi ƙasa zuwa dala 1,740 a cikin watan da ya gabata.
Kafofin yaɗa labarai a Turai sun bayyana cewa ƙwandalar cyrptocurrency ta samu tagomashin farfaɗowa, bayan kamfanoni da cibiyoyi irin su PayPal sun amince su bar kwastomomin su yin hada-hadar kuɗaɗen.
Sannan kuma za su amince wa kwastomomin su na Birtaniya su saya ko su sayar da ‘bitcoin’ da sauran nau’ukan ƙwandalolin ‘cryptocurrency’ daga wannan mako da aka shiga a yau.
Discussion about this post