Jam’iyya tana da mahimmanci a siyasa. Duk da, a kasashen da siyasa ta ci gaba, ba dole bane sai dan siyasa ya tsaya takara a karkashin jam’iya ba. Akwai “independent candidacy”, wanda a lokacin da Farfesa Attahiru Jega yake shugabancin hukumar zabe a Najeriya ya yi kokarin samar da shi. Amma abun bai yiwu ba saboda siyasar kasar Najeriya akwai kurakurai sosai.
A siyasar jam’iya, ana so kowacce jam’iya ta kasance tana da manufofin gaske. Shine abinda ake nufi da ‘manifesto’. Misali, a kasar Amerika, akwai jam’iyar ‘Democratic da Republican’. Wad’annan jam’iyyun, kowacce a cikinsu tana da bayyanannun manufofinta. Hakazalika, jam’iyyun ‘Liberal da Conservative’ a kasar Ingila.
Sanin manufofin jam’iya yana bawa ‘yan kasa damar zabar abunda ya dace da bukatarsu. Tabbas, idan dan siyasa yana da inganci zai yi farin jini a kowacce jam’iya. Mutane sune jam’iya. Kamar yadda rumfa ita ce kasuwa. Hakazalika, bishiya ce take gina daji.
A Najeriya, wasu sun mayar da siyasa babban kasuwanci. Riba kawai su ke hangowa, babu ruwansu da matsalolin wadanda su ka zabesu. Ga irinsu nan a Abuja su na ta gasar siyan kadarori da auren kyawawan mata. To su wadanda su ka mallaka muku kuri’arsu, me ku ka tanadar musu?
Duk dan siyasar da kansa ya waye ya san cewa, kudin da aka same su a siyasa, ba a kashesu a wajen siyasa. Aiki ake yiwa mutane da su, yin hakan ne zai ba ka damar d’orewa a mulki. Ko an qwace maka zabe watarana, idan ka sake tsayawa takara sai ka samu masoya. Watarana zan bada misalan ‘yan siyasa da yawa. Matsoraci ne yake guduwa wata jam’iyar saboda ya samu “job security”
Misali, akwai wani babban dan siyasa a jihar Katsina, duk jam’iyar da ya je sai mutane sun bi shi. A zaben 2011, da karamar jam’iya ya firgita abokan takararsa na babbar jam’iya. Ko me yasa? Ku je ku nemi dalili. Wannan misali ne kawai.
Abin mamaki, Tun yanzu mun fara ganin masu kwad’ayin mulki sun fara canza jam’iya. Abinda zai dinga faruwa kenan, daga nan har zuwa babban za6e a 2023. Shin talaka, ka yadda rayuwarka ta zamo kamar tamola a filin wasa wacce kowa yake buga ta?
Allah ya shiryar da mu.
Discussion about this post