Kashi 73% na daliban da suka rubuta jarabawar WAEC a Katsina sun ci Turanci da Lissafi – Inji Dakta Badamasi

0

Duk da hare-haren ‘yan bindiga da jihar katsina ta ke fama da shi, daliban jihar sun yi nasara a jarabawar WAEC na bana.

Kwamishina Ilimin Jihar Katsina Badamasi Lawal ya bayyana cewa daliban jihar Katsina ba su taba cin jarabawa da yawansu irin yanzu ba, karkashin mulkin gwamna Aminu Masari.

Dakta Badamasi ya bayyana cewa kashi 73 cikin 100 na wadanda suka rubuta jarabawar ne suka ci kiredit a Turanci da Lissafi.

” Daliban jihar Katsina basu taba samun nasara irin haka ba, ace wai dalibai cikin 100 kashi 73 sun yi nasarar cin darussan Turanci da Lissafi. Kafin gwamnatin Masari sai dai kaga kashi 17 cikin 100 ne ke yin nasarar cin turanci da Lissafi a zama daya. Amma tun da muka dare kujerar mulki a 2015 zuwa 2020 hakan ya canja.

Wannan gwamnati ta maida hankali wajen farfado da harkar Ilimi da ya tabarbare a jihar. Hakan ya sa daliban jihar suka samu natsuwa da maida hankali a karatunsa. Gashi tun daga lokacin daliban jihar na samun nasara a jarabawar da suke rubutawa.

Dakta Badamasi ya kara da cewa a zamanin gwamnatin Masari, malaman jihar sun kwankwadi romon gwamnati irin nasu wanda take kula da malamai da tabbatar da sun mori aikin su ta hanyar biyan su alshi a akn lokaci da sauran hakkunan su.

Share.

game da Author