Kasar Saudiyya na kyautata wa Najeriya matuka muna godiya – Sakon Buhari ga Sarki AbdulAziz

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa mahukuntar kasar Saudiyya ƙarƙashin shugabancin Sarki Salman bn AbdulAziz kan yadda ƙasar ke mara wa Najeriya baya musamman wajen karfafa tattalin arzikin kasar.

Buhari ya bayyana haka a lokacin da yake karɓar bakuncin ma ministan harkokin kasashen wajen ƙasar Saudiyya Faisal Bin Farhan Al-Saud a fadar gwamnati a Abuja,

Buhari ya ce a duk lokacin da Najery ke bukatar kasar Saudiyya ta ɗan rage yawan gangar man da ta ke saidawa a kasuwar mai ta duniya domin kuɗaɗen shigar ƙasar ya ƙaru, Saudiyya kan share wa Najeriya hawaye.

” Lallai muna godiya matuka. Kasar Saudiyya na yi mana haksci matuka.

Yarima Faisal Bin Farhan Al-Saud, ya godewa shugaba Buhari na karrama sa da aka yi sannan ya bayyana cewa zai isar wa sarki AbdulAziz da sakƙon shugaba Buhari idan ya koma Saudiyya.

Share.

game da Author