KARA DA KIYASHI ƊAUKAR MARAS SANI: Yadda tsohuwar mata ta ta nemi halaka ni da guba saboda dukiya ta -Basarake Oluwo na Iwo

0

Basarake Oluwo na Iwo da ke cikin Jihar Osun, Abdulrasheed Akanbi ya bayyana yadda matar da ya saki bayan ta zame masa alaƙaƙai ta nemi halaka shi.

Akanbi ya bayyana yadda matar mai suna Chanel Chin ta nemi halaka shi kuma ta kwashe masa kuɗaɗen kwangila.

Basaraken ya fassara shekaru huɗu ɗin da ya yi da matar, wadda kafin ya aure ta, ‘yar ƙwalisa ce kuma sarauniyar kyau, cewa shekaru huɗu ne na kada Allah maimaita, domin zaman ƙarya da zamba ta riƙa kitsa masa.

Haka dai ya bayyana a shafin sa na Instagram. Duk kuwa da cewa bai bayyana sunan ta ba.

Bai fito ya faɗi sunan ta ba, amma dai kowa ya san cewa da tsohuwar matar sa mai suna Chanel Chin ya ke, wadda haifaffiyar ƙasar Kanada ce, kuma ‘ya ga fitaccen makaɗin reggae, Bobo Zaro.

Akanbi ya bada labarin irin yadda ya nuna cewa ya yi murnar samun nasarar rabuwa da shaiɗaniyar da ta dabaibaye shi ta riƙa kwana har kan gadon sa, alhali shi bai san tare da mai neman halaka shi ya riƙa kwanciya ba.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda su ka rabu tun cikin 2019, bayan sun samu saɓanin da basaraken ya ce ba za iya sasantawa ba.

Ya ce ya rabu da matar saboda ta riƙa shirya masa tuggun ɗaukar bidiyon duk wata rayuwar da ya ke yi a cikin ɗakin sa da cikin gidan sa da fadar sa.

Daga nan ta riƙa yi masa barazanar fallasa bidiyon idan bai ba ta maƙudan kuɗaɗe ba.

Idan ba a manta ba ta taɓa yin intabiyu, inda ta zarge shi da kwanciya da ƙaramar yarinya ‘yar shakara 13.

Share.

game da Author