Gawurtaccen kamfanin sarrafa abinci na Nestle, ya bayyana cewa ya ware zunzurutun naira biliyan 535 wadda zai narka a fannin noma, musamman domin samar da abincin da bunƙasa harkokin rayuwar manoman su kan su.
Nestle ya yi wannan sanarwa a birnin New York, yayin taron Majalisar Ɗinkin Duniya Kan Hanyoyin Bunƙasa Abinci a Duniya, wanda ya gudana a birnin New York, na Amurka.
Nestle wanda yanzu haka ke da kamfanonin sarrafa abinci da kayan sha a ƙasashe 22 a duniya, ciki har da Najeriya, ya na da hedikwatar sa ta Najeriya a Ilupeju a Legas.
Babbar masana’antar sa kuma da ake sarrafa abinci da abin sha, ta na Agbara da Shagamu, kan hanyar Legas zuwa Ibadan a Jihar Ogun.
Cikin wata sanarwa da Shugaban Nestle na Duniya, Paul Bulcke ya fitar bayan kammala taron, ya ce Nestle za ta kashe kuɗaɗen a cikin shekaru biyar.
Ya ce sabon tsari ne Nestle zai shigo da shi, wanda ɗimbin jama’a za su amfana a fannin noma, ciki kuwa har da su manoman kan su.
Daga cikin sabon salon da Nestle zai shigo da shi, akwai amfani da tsarin kimiyya da fasaha na zamani a fannin noma, bayar da taimakon fasahar dabarun noma, bayar da tallafi na kuɗaɗe domin bunƙasa noma da kuma da sauran su.
Ya ce tsarin zai Inganta rayuwar manoman karkara matuƙar gaske, har ma da yankuna ko ƙauyukan da su ke rayuwa baki ɗaya.
“A wannan tsari za a yi aiki tare da manoma fiye da 500,000 da masu samar da kayan abinci 150,000 domin ingantawa da bunƙasa wannan sabon tsarin cin moriyar noma da Nestle zai yi, wanda zai samar da abinci.”
Ya ce wannan tsari na ɗaya daga cikin gudunmawar da Nestle zai bayar wurin ganin cewa an cimma ƙoƙarin da ake yi na samar da abinci a ƙarƙashin Shirin Muradin Ƙarni zuwa 2030 a duniya, sai kuma ganin cewa Nestle ya taka rawa wajen daƙile barazanar Canjin Yanayi a duniya, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar da rahoton ƙalubalen da ya ke haifarwa a duniya baki ɗaya.
Nestle sun yi ƙarfi sosai a duniya wajen samar da kayan abincin gwangwani musamman madara da kayan abincin yara.
Su na tu’ammali da harkar kiwon dabbobin da ake tatsa ana yi madara sosai.
Discussion about this post