Tsohon Shugaban hukumar shige da fice ta kasa, Muhammad Babandede, yace shekarar 2023 ta Allah ce, kuma yayi wuri ya bayyana matsayinsa a siyasar Jihar Jigawa.
Babandede yace yana samun kiraye kiraye na ya shigo siyasa amma yace ba sai a siyasa kadai ake taimakawa mutane ba.
Babandede ya bayyana hakan ne yau Lahadi a masarautan Ringim yayinda Sarkin Ringim, Sayyadi Mahmoud, da wasu yan yankin suka hada masa liyafa ta ban girma da nuna godiyarsu bisa taimakawa matasa wajen samun aikin yi a fadin Jihar Jigawa.
A wajen taron na karramawa, Babandede, yace bashi da wani buri a rayuwarsa irin ya taimakawa matasa da kawowa al’ummar sa cigaba irin na zamani.
Yace ba sai a siyasa kawai ba mutum zai iya taimakawa al’ummarsa ba, yace yakamata Yan siyasa su nemi sana’a domin su taimakawa al’ummarsu.
“Alheri da nayiwa mutane lokacin ina shugaban hukumar shige da fice bashi da alaka da siyasa, a rayuwa ba dole bane sai mutum yayi siyasa kafin ya taimakawa mutane.
“Duk wanda ya dauki siyasa sana’a ya kamata yaje ya nemi sana’a saboda siyasa ba sana’a bace kuma ba wajen neman kudi bane, wajen gina al’umma ne, inji Babandede.
Ya kuma cewa yayi shekaru biyar da wata hudu yana Shugabanin hukumar shige da fice, ya kawo cigaba da dama wajen cigaban kasarsa.
Ina godiya ta musanman ga Yan Jigawa, da Gwamna Muhammad Badaru da Sarkin Hadejia Abubakar Maje Haruna da irin goyon baya da suka bane da kuma halartar taron karramani da akayi a garin Abuja, inji Babandede