Dambarwar da ke faruwa a Majalisar Dattawa da ta Tarayya kan batun salon aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo ya ƙi ƙarewa, yayin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ita fa tuni ta samar da ingantaccen tsari kuma sahihi, wanda za ta aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo.
INEC ta jaddada wannan matsaya makonni kaɗan bayan Majalisar Tarayya da ta Dattawa sun ƙi amincewa su bai wa ƙudirin goyon bayan da zai tabbata zuwa cikakkar doka.
PREMIUM TIMES ta bayyana matsayar ‘yan majalisar lokacin gyare-gyaren Dokar Zaɓe.
Yayin da Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da kudirin aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo, ita kuwa Majakisar Tarayya cewa ta yi za ta iya amincewa, amma sai idan Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) da Majalisa sun amince aika sakamakon ta yanar gizo ba zai iya samun tangarɗa ba.
Sau da dama INEC ta sha jaddada cewa a shirye ta ke ta aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo.
Ko a ranar Asabar sai da INEC ta fitar da wata takarda mai lamba No.1/2021kan batun aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo, inda ta jaddada cewa ‘network’ ɗin da Najeriya ke da shi na aika saƙonni ta wayoyin GSM.
INEC ta ce ta na da yaƙinin cewa aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo zai ƙara inganta sahihancin sakamakon. Sannan kuma tattaunawar da aka yi da masu ruwa da tsaki ta nuna lallai jama’a na goyon bayan aika saƙonnin sakamakon zaɓe ta yanar gizo.
Wanann jarida ta buga labarin yadda Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Lawan ya yi kitso da kwarkwata, inda ya naɗa Sanatoci biyar cikin kwamitin duba Ƙudirin Kwaskwarimar Zaɓe, alhali su na adawar kafa dokar aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo.
Shugaban Majalisar Dattawa ya naɗa kwamitin sanatoci bakwai domin su duba inda aka samu dabur-dabur ɗin shawo kan tankiyar da ke tattare da Ƙudirin Kwaskwarimar Dokar Zaɓe.
Cikin Sanatoci bakwai ɗin dai biyar daga cikin su ba su so a riƙa bayyanawa da aika sakamakon zaɓe ta yanar gizo.
Sun kuwa haɗa da Shugaban Kwamitin, Sanata Abdullahi Yahaya, Kabiru Gaya, Ajibola Basiru, Ɗanjuma Goje da kuma Sani Musa.
Sauran biyun masu so a riƙa aikawa da sakamakon zaɓe ta yanar gizo, sun haɗa da Uche Ekwunife sai kuma Mathew Urhoghide.
An ba su aikin haɗuwa tare da kwamitin Majalisar Tarayya domin su duba yadda za a warware tankiyar.
Wuraren da ake tankiya a kai sun haɗa da batu jefa ƙuri’a ta yanar gizo, tantance katin zaɓe ta yanar gizo, sai kuma batun da ya fi tayar da jijiyar wuya a majalisar tarayya da ta dattawa, shi ne batun aikawa da sakamakon zaɓe ta yanar gizo.
INEC ce ta nemi a bi wannan tsari a ƙarƙashin Sashen Dokar Zaɓe ta 52, domin ƙara tsaftace zaɓe.
A lokacin da ake hayaniya kan a amince ko kada a amince da sabon ƙudirin dokar, sanatoci biyar da Lawan ya naɗa su na cikin gungun sanatocin da ba su amince ba, ciki kuwa har da Shugaban Majalisar Dattawa ɗin.
Farkon wannan mako ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga wani ƙorafi da INEC da kuma Yiaga su ka yi, cewar har yanzu Majalisar Tarayya ba ta amince da wasu manyan muradai ba.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ƙungiyar Yiaga Africa sun bayyana cewa har yanzu Majalisar Tarayya ba ta amince da wasu muhimman buƙatu da aka tura mata ba dangane da yi wa Dokar Zaɓe garambawul.
Sun bayyana haka ne a ranar Juma’a a wajen taron masu ruwa da tsaki kan lamarin gyaran Dokar Zaɓe, wanda Yiaga Africa da haɗin gwiwar Majalisar Tallafa wa Tsarin Dimokiraɗiyya a Nijeriya na Tarayyar Turai, wato ‘European Union Support to Democratic Governance in Nigeria Project’ (EU-SDGN) a Abuja.
Babban Kwamishinan INEC kan Yaɗa Labarai, Mista Festus Okoye, wanda Mataimakin Daraktan Tsara Dokoki na INEC, Mista Oluwatoyin Babalola, ya wakilta, ya ce hukumar ta lura da wasu ‘yan matsaloli a ƙudirin yi wa Dokar Zaɓen garambawul duk da yake abuvuwa ne na cigaba.
Okoye ya ce a bisa hakan, hukumar ta kawo shawarar gyararraki kimanin 98 da za a yi wa Dokar Zaɓen amma ba dukkan su aka amince da su ba, misali batun sakin kuɗi da wuri, shirya jadawaɗin aikin rajistar masu zaɓe da wuri, da sauran su, waɗanda ba a amince da su ba tukuna, duk da yake an ɗan samu cigaba.
Ya ce, “Ƙudirin ya ba mu ikon mu yi amfani da na’urar karanta kati mai ƙwaƙwalwa (smart card readers) da sauran kayan kimiyya da zaɓe ta hanyar intanet and amma kuma ƙudirin daga Majalisar Dattawa bai ba mu ikon mu aike da sakamakon zaɓe ba.
“Duk da waɗannan abubuwan, akwai waɗansu sassa da ba a amince da su ba kuma mun yi amanna da cewa idan aka amince da su, zai taimaka wajen haɓaka ingancin zaɓe.
“A Sashe na 68 na Dokar Zaɓe, hukumar ta buƙaci a karɓi shawarar sake nazarin bayyanawa tare sa dawo da sakamakon zaɓe daga jami’an kawo sakamako (returning officers) wanda aka yi ba bisa ƙa’ida ba, kamar misali bayyana sakamakon da aka yi ta hanyar tilastawa a sake duba shi, amna ba a amince da wannan ba.
“Na biyu, mun buƙaci cewa a sauya mana Sashe na 143 na Dokar Zaɓe wanda ya ba suk wani mai cin moriyar zaɓe da aka soke damar ya ci gaba da riƙe muƙami har zuwa lokacin da aka gama shari’ar ɗaukaka ƙara saboda kada mu dinga bada satifiket ɗin amincewa da wanda aka zaɓa mu na kuma sakewa.
“Haka kuma hukumar ta kalli batun aikawa da sakamako a matsayin babban al’amari, hanyar fasaha na ƙara bunƙasa, idan an aika da sakamakon zaɓe, zai inganta sahihancin zaɓe kuma ya rage yin katsalandan, amma ba a amince da waɗannan ɗon ba.’’
Daraktar Shirye-shirye ta Yiaga Africa, Cynthia Mbamalu, ta yaba wa ƙudirin neman garambawul ɗin saboda wani cigaba da aka samu a wasu sassa kamar misali wajen shigar da kalmar da ta shafi jinsi wato “shi ko ita”, da tura kuɗi da wuri don tabbatar da ingancin gudanarwar INEC, sassauƙan tsarin rajistar masu zaɓe, shigo da naƙasassu, da sauran su.
Saboda haka Mbamalu ta yi kira ga shugabannin Majalisar Tarayya da su gaggauta kafa kwamitocin tuntuɓa da za su zauna su fito da ƙasida ɗaya kan ƙudirin yi wa Dokar Zaɓen garambawul kamar yadda aka riga aka zartar.
Mbamalu ta ce ta hanyar yin hakan, ana ba ‘yan majalisar shawarar su sake duba matsayar su kan wasu daga cikib shawarwarin da jama’a da masu ruwa da tsaku su ka kawo masu, waɗanda an tsallake wasu, of ki an siyasantar da su ko sun zama abin muhawara.
Ta ce abu muhimmi shi ne tilas ne kwamitin tattaunawar ya yanke hukunci a bisa muradin jama’ar ƙasa wajen amincewa da gyarw-gyare inda dukkan zaurukan majalisar biyu su ka ɗauki mabambantan ƙudiri don ganin an riƙa yin zaɓuɓɓuka fisabilillahi.
Dakta Ajibola Basiru, shugaban kwamiyin yaɗa labarai na Majalisar Dattawa, ya yaba wa Yiaga Africa saboda tsarin da ta fito da shi, ya ƙara da cewa hanya ɗaya da za a ci gaba da multin dimokiraɗɗa ita ce su tabbatar da cewa akwai nagarta da karɓuwa ga jama’a wajen aikin dimokiraɗiyya wanda shi ne ya kawo mutane zuwa kan dokin shugabanci.