ILLAR TA’ADDANCI: Gwamnantin Tarayya ta fara sake gina makarantu a Yobe

0

Gwamnatin Tarayya ta fara aikin sake gina makarantun da Boko Haram su ka ragargaza a Jihar Yobe da sauran sassan jihohin Arewa maso Gabas.

An fara shirin ne a ƙarƙashin Hukumar Bunƙasa Yankin Arewa-maso-Yamma (NEDC).

Hukumar NEDC dai ta na a ƙarƙashin Ma’aikatar Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwa ta Ƙasa, wacce Minista Sadiya Faruq ke Minista.

Gwamnatin Jihar Yobe dai ta bayar da filaye domin gina makarantu a Potsdam, Buni Yadi (Gujba) da Gashua cikin Ƙaramar Hukumar Bade.

Manajan Daraktan NEDC, Mohammed Alƙali ya bayyana haka a ranar Asabar a Gasua, inda ya ƙara da cewa an bijiro da shirin domin a gaggauta shawo kan ƙarancin makarantu da ajujuwan karatu.

Ya ƙara da cewa matsalar ƙarancin ajujuwan makarantun sakandare da na firamare duk ayyukan ta’addancin Boko Haram ne ya haddasa shi.

Alƙali ya ce Boko Haram sun maida yankin Arewa maso Gabas ya koma yankin da ya fi fatara da talauci a Najeriya. Sannan kuma shi ne koma-baya wajen taɓarɓarewar ilmi.

Ya ce ragargaza makarantun sakandare da na firamare da Boko Haram su ka yi a yankin Arewa maso Gabas ya kawo matsanancin cikas a fannin ilmantar da yara ‘yan firamare da sakandare.

“Hare-haren Boko Haram ta tilasta wa yara aƙalla 600,000 kasa samun damar kammala sakandare da firamare, ko wucewa gaba da sakandare.

“Miliyoyin yara s wannan yanki su na gararamba kan titina, sun kasa samun ilmi.

“Wannan ne dalilin fara gagarimin aikin gina makarantu ya yankin, don a inganta makarantu da ajujuwan da yara za su koma karatu fafur.”

A jawabin sa, Gwamna Mai Mala Buni ya jinjina wa shirin, tare da cewa fara aikin gina makarantun a yanzu ya yi daidai kan kari.

Share.

game da Author