Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola ya bayyana cewa za a gina gadoji guda uku da kuma wasu ƙananan titina (interchange) da masu ƙananan motoci za su riƙa bi domin kauce wa cinkoso a babban titin Legas zuwa Ibadan.
Fashola ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke duba aikin titin a ranar Laraba.
Ya ce idan aka kammala aikin gadojin da ƙananan titinan kauce wa cinkoson, za a samu sauƙi ko ma a kawar da cinkoson motocin baki ɗaya a kan babbar hanyar.
Ya ce, “ganin cewa manyan motoci ne ke haddasa cinkoson, to idan aka kammala gina gadojin uku da titinan kauce wa cinkoso, masu ƙananan motoci, musamman masu yankewa zuwa wuraren ibadu da masu gaggawar zuwa makarantu kamar jami’a, sun samu hanyoyin waske wa duk wani cinkoso kenan. Kuma hakan zai magance cinkoson shi kan sa.”
Wurare uku da ake gina gadojin sun haɗa da Makun, MFM da kuma Lotto (Mowe) duk a kan babban titin Abuja zuwa Ibadan.
Yayin da ya haɗu da Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun a wurin da ake aikin Gadar Lotto, Fashola ya roƙi Gwamna cewa ya na so Gwamnatin Jihar Ogun ta ba Gwamnatin Tarayya damar keta daji da filayen da za a yi aikin, domin aikin ya shigo cikin jihar Ogun.
Ya ƙara da cewa aƙalla a kullum motoci 40,000 na karakaina a kan titin Legas – Ibadan. Saboda akwai wajibcin kawar da cinkoso a kan titin.
Gwamna Dapo Abiodun ya jinjina wa Fashola, kuma ya yi albishir cewa gwamnatin sa a shirye ta ke ta bayar da damar yin ayyukan a jihar ta.